logo

HAUSA

'Yan Najeriya za su fara biyan karin kudin wutar lantarki

2024-04-04 15:58:49 CMG Hausa

 

'Yan Najeriya za su fara biyan karin kudin wutar lantarki bayan karuwar farashin wutar lantarki da hukumar kula da wutar lantarki ta kasar ta sanar a jiya Laraba.

Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya ta aiwatar da gyare-gyare kan farashin wutar lantarki a duk fadin kasar da ke yammacin Afirka, a cewar shugaban hukumar Musiliu Oseni, yayin ganawa da manema labarai a Abuja, babban birnin kasar

Oseni ya bayyana cewa, karin kudin wutar lantarkin ya shafi masu amfani na gida ne, wadanda su ne kashi 15 cikin 100 na al'ummar kasar, amma suna amfani da kashi 40 cikin 100 na wutar lantarki da ake samarwa. Matakin dai na da nufin rage wa gwamnatin kasar nauyin kudi da a halin yanzu take bayarwa na tallafi mai dimbin yawa, na shekarar 2024, wanda ya kai Naira tiriliyan 1.6, kwatankwacin dalar Amurka sama da biliyan 1.2, a cewar Oseni.

Ya kara da cewa, daidaita kudin wutar lantarkin ya zama dole domin a samu ci gaba mai dorewa da kuma samar da wutar lantarki mai inganci, yana mai kira ga ‘yan kasar da su jure matsalar da za ta biyo bayan karin kudin na wucin gadi domin samun fa’ida na dogon lokaci. (Yahaya)