logo

HAUSA

Mu ziyarci titin He da ke birnin Changde na kasar Sin

2024-04-03 10:18:19 CRI

A kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi rangadin aiki birnin Changde na lardin Hunan da ke tsakiyar kasar Sin, kuma ya yada zongonsa na farko a wannan rangadi a titin He na birnin, titin da aka samu tarin al’adun da aka yi gadonsu daga kaka da kakani, ciki har da fasahar dinkin hannu da salon wasan kwaikwayon gargajiya da ake kira Gaoqiang da sassakar katako da sauransu.

A cikin shirinmu na yau, bari mu bi sawun shugaban, mu zanta da wasu daga cikin Magadan al’adun a wannan titi.

Malama Xiao Yao, haifaffiyar lardin Hunan ce, wadda ta yi gadon fasahar dinkin hannu ta gargaijya, nau’in Taoyuan. Da ma abin da malama Xiao Yao ta karanta a jami’a shi ne fasahar dinkin hannu ta lardin Hunan, amma wani kayan dinkin hannu da ta gani wanda aka yi da fasahar dinki ta gargajiya ta Taoyuan ya ba ta matukar sha’awa game da wannan fasahar dinki da ta samo asali daga garinta wato Taoyuan.

Sai dai, fasahar dinkin hannu ta Taoyuan ta kusan bacewa. Domin koyonta, malama Xiao Yao ta ziyarci manyan malamai da wadanda suke sha’awar adana kayayyakin da aka samar ta fasahar dinkin hannu ta Taoyuan, amma a yayin da take kara samun fahimtar fasahar, tana kara damuwa da makomar fasahar. Ta ce,“Yawan wadanda suka yi gadon fasahar dinkin hannu ta Taoyuan bai wuce 7 ko 8 ba yanzu, ciki har da wasu da suka tsufa. Halin da muke ciki yanzu shi ne, ana yawan samun masu sha’awar adana kayayyakin dinkin hannu na Taoyuan, amma su ba su gaji fasahar ba, don haka, akwai matsalar gadon fasahar da ma yayata ta.”

Don haka ma, bayan da ta gama karatu a jami’a, malama Xiao Yao ta koma kauyensu da ke gundumar Taoyuan, kuma a shekarar 2020, ta bude zauren aikin dinkin hannu tare da sa mishi suna Qihui. Tana mai cewa,“Wannan na daga cikin ayyukan farfado da yankunan karkara, kuma mun dauki wasu dalibai da mata dake kusa, don horar da su aikin dinkin hannu, don fatan hada karfinsu wajen aikin farfado da kauyuka.”

Daga nan, sai karin baki masu yawon shakatawa ke zuwa zauren, don koyon wannan fasahar dinki ta gargajiya, tare da samun karin fahimtarta. Har ma yanzu zauren ya zama cibiyar koyon sana’ar dinkin hannu ta Hunan, karkashin kwalejin koyon sana’o’i masu alaka da fasahohi na lardin Hunan. 

Malama Xiao Yao ta ce, a yayin da take gudanar da wannan zauren aikin dinkin hannu, tana kuma wani kokari na yayata fasahar dinki ta Taoyuan zuwa makarantu, ta yadda karin matasa za su samu damar fahimtar fasahar, tare da bada gudunmuwa ga aikin kare fasahar da yayata ta da ma sabunta ta.

Malama Xiao Yao tana kuma fatan za a kara hada al’adun da aka yi gado da harkar yawon shakatawa, ta yadda al’adun za su kara wa yawon shakatawa ma’ana da armashi, a yayin da kuma yawon shakatawa zai taimaka wajen kara yayata al’adun.

A titin He da ke birnin Changde, akwai wani sanannen ginin gargajiya, inda a kan yi wasan kwaikwayon gargajiya mai salon Gaoqiang.

Tuni a shekarar 2006, aka sanya salon wasan cikin jerin al’adun gado na kasar Sin.

Idan muka tabo wasan kwaikwayo mai salon Gaoqiang, akwai wata ‘yar wasan da bai kamata a manta da ita ba, kuma ita ce Peng Ling, mai gadon wasan kwaikwayon gargajiya na salon Gaoqiang na Changde, wadda ta taba samun lambar yabo ta koli ta kasar Sin, a fannin wasan kwaikwayo.

Iyayenta ma ‘yan wasan kwaikwayo ne da sunansu ya karade birnin Changde, wadanda suka yi tasiri sosai a kanta. Malama Peng Ling ta ce,“Na girma ne a kungiyar ‘yan wasan kwaikwayo, inda na gane ma idona yadda tsoffinmu suka tsaya ga gadon al’adun wasan kwaikwayo. A lokacin, su kan kwashe kayansu su je kauyuka su yi wasanni, duk da wahalar da suka fuskanta.”

A shekarar 1979, makarantar koyon fasahohi ta lardin Hunnan ta kafa sashen koyon wasan kwaikwayon Han a birnin Changde, kuma Peng Ling wadda a lokacin ke da shekaru 11 da haihuwa, ta zama daya daga cikin rukunin dalibai na farko a sashen. Ya zuwa shekarar 1984, Peng Ling ta kama aiki da kungiyar wasan kwaikwayon gargajiya ta Han a birnin Changde, har ma ta zama abokiyar aikin iyayenta. Amma ba a jima ba kafin ‘yan wasa da dama su bar aikin, sakamakon dan kudi kadan da bai taka kara ya karya ba da ake samu a aikin. Peng Ling ta ce,“A lokacin, abokan aikinmu da yawa sun bar aikin, amma a lokacin, iyayena sun ce min, bai kamata ki bar aikin da kika zaba kuma kike kishinsa ba. Al’adun gargajiya abu ne da muka gada daga kaka da kakaninmu, wadanda bai kamata mu bari ba.”

Kwalliya ta biya kudin sabulu. A shekarar 2004, Peng Ling ta samu lambar yabo ta Plum Performance Award, wato lambar yabo ta koli a kasar Sin a fannin wasan kwaikwayon gargajiya.

A ganin Peng Ling, nauyin da ya rataya a wuyan ‘yan wasan kwaikwayon gargajiya da ma sauran masu aikin da ya shafi al’adu shi ne, su yi gadonsu. Bisa ga kokarin da ta yi, karin matasa sun fara kaunar wasan kwaikwayon, har ma sun kama wannan aikin.

Kamar yadda muka bayyana a farkon shirin, titin He ya kasance zango na farko da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yada a rangadin aiki da ya kai birnin Changde a kwanan baya, inda ya yi nuni da cewa, birnin Changde birni ne da yake da arzikin al’adun gado, kuma ya kamata a yayata su da kuma raya su yadda ya kamata a zamanin da muke ciki. Zhang Jinling na daga cikin wadanda ke bin malama Peng Ling wajen koyon wasan, ta bayyana cewa, “Yanzu haka gwamnati na dora matukar muhimmanci a kan al’adun gargajiya, musamman ma al’adun gargajiya na wurare daban daban na kasar, kuma hakan ya ba mu masu wannan aikin kwarin gwiwa matuka.”