logo

HAUSA

Sin ta harba sabon tauraron dan Adam da ake iya sarrafawa daga nesa

2024-04-03 09:15:46 CMG Hausa

A yau Laraba, kasar Sin ta harba tauraron dan Adam da ake iya sarrafawa daga nesa ta hanyar amfani da rokar Long March-2D.

Rokar ta tashi ne da misalin karfe 6:56 na safiya agogon Beijing, daga cibiyar harba taurarin dan Adam ta Xichang dake lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar Sin, inda ta harba tauraron Yaogan-42 01 zuwa sararin samaniya tare da shiga falakinsa da aka tsara.

Wannan shi ne karo na 515 da aka yi amfani da dangin rokar Long March wajen gudanar da wannan aiki. (Fa’iza Mustapha)