logo

HAUSA

Shugaban addini na kasar Iran: Za a hukunta kasar Isra'ila

2024-04-03 11:00:47 CMG Hausa

Shugaban koli na addini na kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei, ya yi Allah wadai da kakkausan harshe kan harin da kasar Isra'ila ta kai gidan jakadancin kasar Iran dake kasar Syria ta amfani da makamai masu linzami.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata, Ayatollah Khamenei ya kuma yi alkawarin za a hukunta kasar Isra'ila bisa "aikace-aikacen karya doka" da ta yi. 

Labarin da kamfanin dillacin labarai na kasar Iran IRNA ya gabatar ya nuna cewa, a daren ranar 1 ga wata bisa agogon wurin, an kira taron kwamitin koli na tsaron kasar Iran, inda aka yanke shawara game da matakan da za a dauka dangane da harin da aka kai gidan jakadancin kasar. Manyan jami’an da suka halarci taron sun hada da shugaban kasar Iran Seyed Raisi, da babban magatakardan kwamitin koli na tsaron kasar, Ali Ahmadian, da sauransu.

Ban da haka, ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta sanar a jiya Talata cewa, ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian ya yi hira ta wayar tarho da babban sakataren MDD Antonio Guterres a ranar, inda Abdollahian ya ce kasar Iran na fatan ganin MDD ta yi Allah wadai da matakan "ta'addanci" da kasar Isra'ila ta aiwatar, da bukatar kwamitin sulhu na Majalisar da ya kira taron gaggawa dangane da harin. A nashi bangare, Mista Guterres ya ce MDD tana Allah wadai da duk wani hari kan hukumomin diplomasiyya da jami'ansu.

Kasar Isra'ila ta kai harin makamai masu linzami kan ginin sashen kula da 'yan kasar Iran dake Syria, wanda ke cikin farfajiyar gidan jakadancin kasar Iran a kasar Syria, a ranar Litinin. Bisa rahoton da IRNA ya gabatar, harin ya haddasa asarar rayukan mutane 13. Bayan abkuwar lamarin, dimbin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sun yi Allah wadai da mummunan harin. (Bello Wang)