logo

HAUSA

Starlino: Kaina ya kara wayewa a kasar Sin

2024-04-03 09:18:24 CMG Hausa

Kasashen Sin da Zambiya na da kyakkyawar abota. Akwai wani matashin kasar Zambiya, wanda ya yi tafiya mai nisa don zuwa kasar Sin, saboda kaunarsa ga kasar, inda ya zo birnin Xi’an dake lardin Shannxi don karatu da raya sana’a. A cikin shirinmu na yau, za mu ji ta bakin wannan matashi dan kasar Zambiya mai suna Starlino, za mu ji labari game da kansa da kasar Sin.