logo

HAUSA

An rantsar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin shugaban Senegal

2024-04-03 09:30:27 CMG Hausa

Sabon shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye, ya sha rantsuwar kama aiki na tsawon wa’adin shekaru 5, jiya Talata a Diamniadio dake da nisan kilomita 30 daga Dakar, babban birnin kasar.

Bikin rantsuwar ya samu halartar shugabannin kasashen yankin da dama.

Da yake jawabi yayin bikin, shugaba Faye ya ce, “A tare da takwarorina na Afrika, ina tabbatarwa Senegal kudurina na karfafa kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali da dunkulewar Africa.”

Ya kara da cewa, “Ga sauran kasashe kawaye da abokan hulda, ina nanata kudurin Senegal na bude kofarta ga musaya bisa mutunta cikakken ‘yancinmu da cimma burikan al’ummarmu karkashin hadin gwiwar moriyar juna.”

Bassirou Diomaye Faye, ya yi nasara ne a zagayen farko na zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 24 ga watan Maris, bayan ya samu kaso 54.28 na kuri’un da aka kada, inda ya zama shugaban Senegal na 5, tun bayan samun ‘yancin kan kasar a shekarar 1960. (Fa’iza Mustapha)