logo

HAUSA

Gabon ta kaddamar da taron tattaunawa na kasa domin aiwatar da gyare-gyare

2024-04-03 13:55:44 CMG Hausa

Kasar Gabon ta kaddamar da taron tattaunawa kan batutuwan kasa, domin lalubo hanyar aiwatar da gyare-gyare da gudanar da zabuka.

Shugaban rikon kwarya na kasar Brice Clotaire Oligui Nguema da shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera, sun halarci kaddamar da taron jiya Talata a birnin Libreville.

Yayin taron, mahalarta za su tsara rukunonin daban-daban da za su tsara daftarin kundin tsarin mulkin kasar, wanda za a kadawa kuri’ar raba gardama kafin amincewa da shi. Tattaunawar wadda aka tsara kammalawa a ranar 30 ga watan Afrilu, za ta kuma shafi batun gyara dokokin zabe. (Fa’iza Mustapha)