logo

HAUSA

Yadda kasar Sin ke bayar da gudummawar bunkasa tattalin arzikin duniya

2024-04-03 08:02:42 CMG Hausa

Yayin da tattalin arzikin duniya ke fuskantar tarin kalubale, tafiyar hawainiya da rashin tabbaci, kasar Sin a nata bangare tana ta samar da sabbin damammaki ga sassan kasuwanni na duniya, da ma raba dabarunta na raya tattalin arziki, wanda hakan ya zamo babbar gudummawa da Sin din ke baiwa ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya. 

Bayan da tattalin arzikin kasar Sin ya shiga wannan shekara ta 2024 cike da karsashi, da daidaiton ci gaba, masana da dama a fannin tattalin arziki da jagororin kasuwanci, na bayyana kyakkyawan fata ga bunkasar tattalin arzikin Sin da ci gaban kasar baki daya.

Yayin da Sin ke kara zamanantar da birane, da daga matsayin masana’antu, sashen ci gaban fasahohi na dijital, da samarwa, da amfani da makamashi maras gurbata muhalli na kara samar da sabbin hidimomi da fadada kasuwannin makamashi.

Ko shakka babu, ta hanyar gabatar da dandalolin bunkasa ci gaba tsakanin sassa daban daban na duniya, kasar Sin na kara samar da sabbin damammaki na cimma moriyar juna ga kasa da kasa, da shigar da sabon kuzari da karfin ingiza tattalin arzikin duniya gaba. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Faeza Mustapha)