logo

HAUSA

Abincin Malatang na taimakawa ci gaban tattalin arzikin wani birni dake arewa maso yammacin kasar Sin

2024-04-02 17:35:29 CMG Hausa

Tianshui, wani birni ne na lardin Gansu dake arewa maso yammacin kasar Sin. A ‘yan kwanakin nan, wani nau’in abinci mai suna Malatang, wato romon kayan lambu mai yaji na jan hankalin masu yawon bude ido da dama daga duk fadin kasar Sin, al’amarin da ya taimaka sosai ga habakar tattalin arzikin wurin.