Rasha: Mutane 4 da aka cafke a Dagestan na da alaka kai tsaye da harin Moscow
2024-04-02 11:21:25 CMG Hausa
Hukumar tattara bayanan sirri ta kasar Rasha (FSB) ta bayyana a jiya Litinin cewa, mutane 4 da aka cafke ranar Lahadi a Jamhuriyar Dagestan ta kasar bisa zargin ta’addanci, na da alaka kai tsaye da harin da aka kai zauren kide-kide na Crocus City dake birnin Moscow.
Wata sanarwa da FSB ta fitar ta bayyana cewa, wadanda ake zargin, sun samar da kudi da makamai ga maharan. Kana ana zarginsu da kitsa harin ta’addanci a wani wurin shan iska a birnin Kaspiysk.
Cikin wani bidiyo da FSB ta wallafa, daya daga cikin mutanen ya tabbatar da cewa ya dauko makamai daga birnin Makhachkala tare da mika su ga maharan zauren kide-kiden.
An cafke mutanen 4 ne a biranen Makhachkala da Kaspiysk dake Dagestan a ranar Lahadi, yayin wani samame na musammam na yaki da ta’addanci.
An kuma samu makamai masu sarrafa kansu da albarusai da hadaddun ababen fashewa, a wurin da aka cafke mutanen. (Fa’iza Mustapha)