logo

HAUSA

Alkaluman sun shaida hasashe mai kyau da aka yi wa tattalin arzikin kasar Sin

2024-04-02 11:18:40 CMG Hausa

A baya bayan nan, manyan ma’aunai uku na tattalin arzikin kasar Sin sun karu tare, abun da ya ja hankalin kasashen waje sosai. A ganin kafofin watsa labaran kasashen waje, ciki har da kamfanin dillancin labarai na Faransa wato AFP, wadannan alkuluman da suka zarce hasashen da aka yi, alamomi ne masu dumi-dumi na karuwar saurin farfadowar tattalin arzikin Sin, lamarin da ba kara wa mutane kwarin gwiwa kadai ya yi ba, har ma da zuba sabon kuzari ga tattalin arzikin duniya.

Idan aka kwatanta da makamancin lokacin a watan da ya gabata, alkaluma masu dumi-dumi da sassan gwamnatin Sin suka bayar a watan Maris na bana sun nuna cewa, ma’aunin kayayyakin da masana’atu ke sayarwa na PMI ya kai kashi 50.8 cikin dari wato karuwar kashi 1.7 cikin dari, kana ma'aunin ayyukan kasuwanci da ba na masana’antun samar da kayayyaki ba, ya kai kaso 53 cikin dari, karuwar kashi 1.6 cikin dari, haka ma hadadden ma’aunin samarwa da fitar da kayayyaki na PMI ya kai kashi 52.7 cikin dari, karuwar kashi 1.8. 

Game da wannan, kamfanin dillancin labarai na Bloomberg na Amurka da sauran kafofin watsa labaran kasashen duniya sun bayyana cewa, alkaluman sun nuna makoma mai kyau ta masana’antun samar da kayayyaki na Sin, haka kuma sun nuna cewa tattalin arzkin kasar yana gudana yadda ya kamata..

Me ya sa tattalin arzikin Sin ya samu irin wannan tagomashi? Wani mai binciken harkokin tattalin arziki ya bayyana cewa, ban da karuwar bukatu na cikin gida da tallafin bukatu na waje, an dogara ga manufofin da gwamnatin Sin ta tsara don kyautata yanayin tattalin arziki, da habaka bukatun cikin gida da kuma kiyaye yanayin cinikin waje.

Kazalika, ma’aunin samar da kayayyaki, da ma’aunin sabbin kwangiloli, da kuma ma’aunin cinikin shige da fice, sun yi kyau a watan Maris, wanda ke nufin yanayin tattalin arzikin Sin na kyautatuwa, haka kuma yana tafiya kan hanyar ci gaba lami lafiya. Mai binciken ya kara da cewa, wannan ya nuna saurin karuwar GDPn a rubu’in farkon bana na da kyau, wanda ya aza harsashi ga cimma burin karuwar tattalin arziki na kashi 5 cikin dari a shekarar nan.

Babban mai nazari na cibiyar Brookings, Christopher Thomas, ya bayyana cewa, Sin na kara saurin bunkasa sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, kuma wannan zai sa sakamakon kirkire-kirkire da aka samu ya kawo alheri ga duk fadin duniya, lamarin da zai kara sabon kuazari ga tattalin arzikin duniya.(Safiyah Ma)