logo

HAUSA

Iran ta lashi takobin mayar da martani kan harin Isra’ila a ofishin jakadancinta dake Syria

2024-04-02 10:29:34 CMG Hausa

Jakadan Iran a Syria, Hossein Akbari ya lashi takobin kasarsa za ta mayar da martani mai karfi kan harin da Isra’ila ta kai ofishin jakadancinta dake birnin Damascus na Syria a ranar Litinin.

Hossein Akbari ya shaidawa manema labarai bayan aukuwar harin makami mai linzami da Isra’ila ta harba kan ginin ofishin jakadancin kasarsa cewa, harin ya yi sanadin mutuwar abokan aikinsa 5, yayin wasu masu tsaron ofishin 2 suka jikkata.

Ya ce a bayyane yake cewa Isra’ila ta keta dokokin kasa da kasa. Yana mai tambayar yaushe hukumomin kasa da kasa dake da alhakin aiwatar da wadannan dokoki za su dauki mataki?

A nasa bangare, ministan harkokin wajen Syria Faisal Mekdad, wanda ya je wurin da lamarin ya auku, ya yi tir da harin, yana mai cewa bai kamata ba.

A cewar ma’aikatar tsaron Syria, harin na makami mai linzami ya auku ne da misalin karfe 5 na yamma agogon kasar, lokacin da Isra’ila ta kaddamar da hari kan ginin ofishin jakadancin Iran ta sama, daga yankin tuddan Golan da ta mamaye. (Fa’iza Mustapha)