logo

HAUSA

Ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a watannin farkon bana zai kara karfafa gwiwa a duniya

2024-04-02 19:54:38 CMG Hausa

A baya-bayan nan, sassan gwamnatin kasar Sin sun fitar da alkaluma game da ma’aunan tattalin arziki 3 da suka hada da na yawan kayayyakin da masana’antu ke sayarwa, da na bangaren kasuwanci da bai shafi samar da kayayyaki ba, da kuma na samarwa da fitar da kayayyakin, wadanda suka karu da kaso 1.7 da 1.6 da 1.8 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.

Na tuna yadda a lokacin da gwamnatin kasar Sin ta gabatar da rahoton aiki da bayyana burinta na samun karuwar tattalin arziki da kaso 5 a bana, na ji da kunnena wasu kafafen yada labaran yammacin duniya na cewa, kasar Sin ba ta bayyana yadda za a yi ta samu wannan ci gaba ba. Wato kamar su na ganin wannan burin ba mai yuwuwa ba ne. Amma wadannan alkaluma da aka gabatar sun nuna cewa, kasar Sin ta san abun da take yi kuma ta na da yakinin cimma burikan da ta sanya a gaba. A matsayin wadda ta shafe shekaru a kasar Sin, na san kasar ba ta sanya burin da ba za ta iya cimmawa ba, ko in ce, ban ma taba ganin ta sanya wani buri da ta gagara cimmawa ba.

Ci gaban da Sin ta samu cikin wadannan watanni, bai tsaya kadai ga wadannan ma’aunai 3 ba, an kuma samu bunkasar wasu manyan fannoni kamar na samar da hidimomi da rayuwar al’umma da sayyaya da sauransu. Abun da irin wadancan kafofin watsa labarai da na bayyana a baya ba su gane ba shi ne, tattalin arzikin kasar Sin na bisa tubali mai kwari dake da juriya. Haka kuma, kasar ba ta dogara da kasashen waje wajen raya tattalin arzikinta ba, domin kasar Sin ta mayar da hankali ne wajen amfani da albarkatun da ta mallaka a cikin gida da kyawawan dabarun da suka dace da ita, da kuma fasahohi da karfinta na kirkire-kirkire. Misali, a cikin bangarorin da suka samu ci gaba, akwai rayuwar al’umma da karuwar sayayya a cikin gida. Kyautatuwar rayuwar al’umma na nufin samun kwanciyar hankali da biyan bukatu da kuma samuwar wadata. Samuwar wadata kuma shi ne ke kara ingiza sayyaya da kashe kudi a cikin gida, wanda ke bayar da gudunmuwa ga tattalin arziki. A ganina, wadannan ci gaba da aka samu cikin kankanin lokaci, somin tabi ne na irin ci gaban da za a kai ga cimmawa zuwa karshen shekara. Haka kuma, ba kasar Sin kadai za ta amfana ba, domin wannan sakamako da aka samu a lokaci kalilan, ba karfafa gwiwar duniya kadai zai yi ba, har ma da samar da makoma mai haske ga tattalin arzikin duniya kamar yadda ya saba.(Fa'iza Mustapha)