logo

HAUSA

Hadin gwiwar Afirka da Sin a fannin yanar gizo na kyautata rayuwar jama'a

2024-04-02 16:06:57 CMG Hausa

by Bello Wang

Abokaina, bari mu yi tunanin abkuwar wani batu: A cikin wani kauye dake wata kasa ta nahiyar Afirka, wani yaro ya kamu da zazzabi da tsakar dare, amma likita ba zai samu damar zuwa gidan yaron cikin gaggawa ba, saboda yana zaune a cikin gari. Amma iyayen yaron ba su damu ba, maimakon haka sai suka bude wata manhaja (APP) dake cikin wayar salula, da rubuta bayanin halin da yaron ke ciki kan APP din. Sa'an nan bayan kimanin minti 10, sai wani karamin jirgin sama maras matuki ya sauka a gaban kofar gidansu, dauke da maganin da yaron ke bukata.

Hakika wannan batun da muka yi tunani ya riga ya zama gaskiya. Wani saurayi dan kasar Zambia mai suna Clivate Maiba ya koyi dabarar amfani da dandalin sarrafa na’urorin zamani a kasar Sin, sa'an nan ya bude wani kamfanin samar da hidimar jinya a kasarsa ta Zambia, inda ake gwada yin amfani da fasahar zamani wajen sarrafa jirgin sama maras matuki, don kai magani, da jini, da alluran rigakafi da ake bukata, ga likitoci da daidaikun mutane da ke zama a yankunan karkara marasa hanyoyi masu inganci.

Wannan misali ya nuna yadda hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin ta fuskar yanar gizo ko Internet da fasahohin zamani ke haifar wa matasan kasashen Afirka damammakin kaddamar da sabbin sana'o'i, sa'an nan an samar da taimako ga masu raunin tattalin arziki dake nahiyar Afirka a fannin kyautata zaman rayuwarsu.

A yau Talata an gudanar da wani dandalin tattauna damar hadin gwiwa kan ci gaban yanar gizo ko Internet, tsakanin bangarorin Afirka da Sin, a birnin Xiamen na kasar Sin, inda jami'ai da 'yan kasuwa na bangarorin 2 suke mai da hankali kan damar hadin kansu, a fannonin tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani, da kafofin yada labaru na yanar gizo, da tsaron yanar gizo, da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI, da dai sauransu, gami da tattauna dabarar yin amfani da yanar gizo da fasahohin zamani wajen kyautata zaman rayuwar jama’a, kamar dai yadda misalin kasar Zambia da na gabatar muku ya nuna.

Cikin shekarun nan, an samu dimbin nasarori a hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, a fannin yanar gizo ko Internet. Misali a bangaren gina kayayyakin more rayuwa, ya zuwa karshen shekarar 2021, kasar Sin ta gina fiye da kashi 50% na tashoshi da yanar gizo mai sauri na wayar salula, gami da shimfida kananan wayoyin aika sako ta haske fiye da tsawon kilomita dubu 200, a kasashen Afirka. Kana a fannin ciniki ta yanar gizo, sama da rabi na yawan cinikayyar yanar gizo da ake yi a kasuwannin gabashin Afirka an yi su ne ta dandalin ciniki na Kilimall da wani basine ya kafa, inda yawan mutanen da suke amfani da dandalin ya zarce miliyan 10. Sa'an nan a fannin hada-hadar kudi, kamfanin Opay na kasar Najeriya ya shigar da jari da fasahohi daga kasar Sin, ta yadda ya zama daya daga cikin kamfanonin hidimar biyan kudi mafi girma a kasar Najeriya. A sauran fannoni irinsu horar da ma'aikata, da tsaron yanar gizo ma, ana samun yanayi kusan iri daya. Za a iya cewa a kusan dukkan sana'o'i masu alaka da fasahohin yanar gizo na galibin kasashen dake nahiyar Afirka, ana iya ganin yadda fasahohi da jarin kasar Sin ke taka muhimmiyar rawa.

Za a so a yi tambaya cewa, me ya sa kasar Sin ce ke taka rawa a fannin? Kuma don me ake son hadin gwiwa da kasar Sin, yayin da ake neman raya sana'o'i masu alaka da yanar gizo ko Internet?

Dalilin shi ne, da farko, fasahohin kasar Sin a fannin yanar gizo su ne a kan gaba a duniya.

An kammala aikin gina kayayyakin more rayuwa masu alaka da fasahohin sadarwa mafi girma a duniya, a kasar ta Sin, ta yadda ko a cikin kauyukan kasar ma, ana samun ingantaccen tsarin sadarwa. Ban da haka, kasar ita ta fara rungumar fasahar sadarwa mai ci gaba ta 5G, inda a karshen shekarar 2023, yawan al'ummar kasar masu wayoyin salula dake aiki da 5G ya kai miliyan 805. Ban da haka, kasar Sin ta kware a fannin kirkirar sabbin fasahohi, abin da ya sa ta kan gaba a duniya a fannonin mallakar fasahohi masu alaka da na'urorin kwaikwayon tunanin dan Adam, da aikin tsara karamin kayan latironi na Chip, da dai sauransu.

Kana dalili na biyu shi ne, akidar kasar Sin ta fuskar hadin kai tare da kasashen Afirka ta gaskiya, da kauna, da sahihanci, gami da samar da sakamako na zahiri, ta sa kasar yarda da gabatar da ingantattun fasahohi, da damammakin raya kasa, ga bangarorin Afirka. Cikin shawarar kafa al’umma mai makomar bai daya a fannin yanar gizo bisa hadin gwiwar Sin da Afirka, da kasar Sin ta gabatar, kasar ta yi alkawarin taimakawa kasashen Afirka wajen gina kayayyakin aikin sadarwa, da kula da yanar gizo, da sayar da kayayyaki ga kasuwannin Sin ta hanyar cinikin yanar gizo, da kuma rage talauci ta hanyar amfani da fasahohin zamani.

Idan muka leka kasar Sin, za mu ga yadda yanar gizo ko Internet ta shafi dukkan bangarorin rayuwar jama’ar kasar, irinsu sayayya, da biyan kudi, da hulda da abokai, da karatu, da ganin likita, da gudanar da taro, da sayar da kayyayaki ta hanyar watsa bidiyo kai tsaye, da dai sauransu. Ta wayar salula, kusan za a iya tafiyar da dukkan al’amuran yau da kullum a kasar. To, wannan irin saukin rayuwa, da saurin ci gaba da fasahohin zamani suke haifarwa tattalin arziki, da zaman al’umma, su ne abubuwan da kasar Sin ke son morewa tare da jama’ar kasashen Afirka, ta hanyar gudanar da hadin gwiwa tsakanin bangarorin 2. (Bello Wang)