Nijar na sake farfado da wuraren noman gandari da ke iyaka da Najeriya, domin neman ‘yancin kanta ta fuskar abinci
2024-04-02 13:53:01 CMG Hausa
A jamhuriyar Nijar, ministan noma da kiwo, kanal Mahamane Elhadj Ousmane, ya kaddamar a hukumance a wannan mako, da ayyukan gyara wuraren noman rani da na cibiyar bunkasa noma da ke yankin Diffa mai iyaka da tarayyar Najeriya.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya hada mana da wannan rahoto.
A Nijar ta yau, babban burinmu da ya zama dole, bisa la’akari da abin da muka fuskanta a tsawon watannin baya bayan nan, shi ne neman ‘yancin gashin kanmu ta fuskar abinci, domin kaucewa duk wani dogaro da wasu kasashe, a cewar ministan noma da kiwo, kanal Mahamane Elhadj Ousmane a lokacin bikin kaddamar da katafaren aikin farfado da wuraren noman gandari ko noman rani da ke yankin Diffa.
A cewar kamfanin dillancin labarai na kasa ANP da ke rawaito kalaman ministan, Nijar na fatan gani tare da wadannan wurare samun wata karuwa a fannin noman shimkafa da alkama.
Noman shimkafa, da yanzu yake ton 307 zai wuce zuwa ton 3328, a yayin da noman alkama da ke ton 68 zai cimma ton 360, a cewar ministan noma da kiwo na kasar Nijar.
Kudaden farfado da wadannan wuraren noman gandari ko noman rani za su fito daga kasafin kudin kasa da kuma na asusun zumunci da ceton kasa na FSSP wajen fiye da sefa miliyan biyu.
Kuma wadannan kudade za su shiga kai tsaye wajen gyaran dukkan gine gine da suka shafi noman gandari ko noman rani da kula da batsewar ruwan Komadougou Yobe da ke fitowa daga tafkin Chadi.
Mamane Ada, sashen Hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.