logo

HAUSA

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kaiwa Ofishin Jakadancin Iran Dake Syria

2024-04-02 20:06:45 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin ta yi Allah wadai da harin da aka kaiwa ofishin jakadancin Iran dake kasar Syria, kuma ko kadan bai dace a keta hurumin tsaron cibiyoyin diflomasiyya ba.

Wang Wenbin, wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, yayin taron manema labarai da ya gudana a birnin Beijing ya kara da cewa, wajibi ne a martaba ikon mulkin kai na Syria, da ‘yanci da tsaron yankunanta, kuma Sin na adawa da duk wani mataki da zai kai ga rura wutar zaman dar-dar a yankin Gabas ta Tsakiya. (Saminu Alhassan)