logo

HAUSA

Harin Isra’ila a Gaza ya yi sanadin mutuwar ma’aikatan agaji 5

2024-04-02 14:52:38 CMG Hausa

Akalla ma’aikatan kungiyar agaji ta WCK 5 ne suka mutu yayin da suke tafiya cikin mota a birnin Deir al-Balah dake tsakiyar zirin Gaza, biyo bayan wani hari ta sama da Isra’ila ta kai birnin.

Wata sanarwa da ofishin yada labarai dake karkashin gwamnatin Hamas ya fitar, ta ce ma’aikatan agajin sun hada da baki 4 da dan Palasdinu 1. Tana mai cewa suna aikin rangadi ne a tashar ruwa da za ta karbi wani sabon kashin kayyayakin agaji.

A nata bangare, rundunar sojin Isra’ila ta ce tana gudanar da cikakken bincike domin tantance aukuwar mummunan lamarin.

WCK, kungiya ce mai zaman kanta dake samar da abinci yayin da ake fama da ibtila’i. (Fa’iza Mustapha)