logo

HAUSA

Sabuwar gwamnatin Palasdinu ta yi rantsuwar kama aiki

2024-04-01 10:57:37 CGTN HAUSA

 

Sabuwar gwamnatin Palasdinu karkashin jagorancin firaminista Mohammad Mustafa, ta yi rantsuwar kama aiki, jiya Lahadi da dare a birnin Ramallah dake yammmacin gabar kogin Jordan.

Labarin da kafar yada labarai ta Palasdinu ta bayar ya ruwaito cewa, sabuwar gwamnatin na kunshe da ministoci 23, kuma 6 daga cikinsu Palasdinawa ne ‘yan asalin yankin Gaza. Haka kuma, ban da mukamin firaminista, Mohammad Mustafa shi ne ministan harkokin waje.

A ranar 26 ga watan Fabrairu, shugaban Palasdinu Mahmoud Abbas ya amince da murabus na firaminista na waccan lokaci Mohammad Shtayyeh, inda ya nemi Shtayyeh ya sauke nauyin dake wuyansa kafin a kafa sabuwar gwamnati. A ran 14 ga watan Maris kuma, Mahmoud Abbas ya baiwa Mohammad Mustafa umurnin kafa sabuwar gwamnati, kana a ran 28 ga watan da ya gabata, Mustafa ya gabatar da shirinsa, wanda ya samu amincewa daga shugaba Abbas. (Amina Xu)