logo

HAUSA

Lokaci ya yi da kasashen yamma za su yi watsi da tunanin wai sun fi sauran kasashe

2024-04-01 21:08:40 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

Kwanan baya, wakilin kafar yada labarai ta BBC Steve Rosenberg ya gabatar da wani shirin bidiyo ta kafar sada zumunta ta X, inda ya zanta da wasu mutanen Rasha game da batun “ko an gudanar da babban zaben kasar Rasha cikin ‘yanci da adalci?” A yayin da babbar editar gidan talabijin na RT, Margarita Simonyan, take amsa tambayar “shin kina ganin akwai abokin takara mai karfi a zaben?” , ta amsa da cewa, “Ko akwai bukatar hakan? Me ya sa?” “Me ya sa kullum kuke ganin tsarin rayuwarku ya fi namu? Har da yadda kuke tambayoyi da abubuwan da kuke yi. Ku kan yi tambaya kamar ‘me ya sa ku ba ku yi abu kamar yadda muka yi ba?’ Sabo da mu ba ku ba ne, kuma mu ma ba mu son ku...”  

Sai kuma wani shirin da BBC ya fitar na zantawa da shugaban kasar Guyana, Mohamed Irfaan Ali, wakilin BBC Stephen Sackur ya nuna shakku game da yadda kasar Guyana ke kara samar da man fetur da iskar gas a cikin ‘yan shekarun baya, hakan a cewarsa zai kara fitar da iskar Carbon. Shugaban Guyana a nasa bangaren ya bayyana cewa, kasashen yamma ba su da iznin yi wa Guyana lacca a kan batun kiyaye muhalli. A cewarsa, Guyana na bukatar yin amfani da albarkatun mai da iskar gas da take da su wajen bunkasa tattalin arzikinta, a sa’i daya, yawan dazuzukan da aka sare a Guyana shi ne mafi karanci a duniya, “ko da mun kai iyakar bunkasa albarkatun mai da gas da muke da su, za mu kai ga zuke dukan iskar Carbon da muka fitar…A cikin shekaru 50 da suka wuce, an rasa kaso 65% na mabambantan halittu a duniyarmu, amma mun kiyaye mabambantan halittu, shin kun ba wannan batun muhimmanci? Yaushe ne kasashe masu sukuni za su biya kudi domin hasarorin da aka yi?”

A hakika, kasashen yamma sun dade suna daukar abin da suke so a matsayin ma’auni daya tilo na tabbatar da abubuwan da ke wakana a duniya su kasance mai kyau ko a’a, wato a ganinsu, komai nasu ya fi na sauran kasashe, kuma muna iya ganin hakan a tambayoyin da wakilan BBC suka yi, kamar “Akwai matsala a zabenku, sabo da ya sha bamban da namu.” “Ba ku da ‘yancin bunkasa kanku, sabo da hakan zai lalata muhallin duniya.”

A zamanin baya, domin fadada mulkin mallaka a duniya, kasashen yamma suka bambanta kasashen duniya, wato da na yammaci da wadanda ba na yammaci ba, tare da bayyana kasashen yamma a matsayin masu wayewar kai da ci gaba, wadanda ba yammaci ba kuma a matsayin marasa wayewar kai da koma baya, don wanke laifukan da suka yi na babakere da ma hare-hare. Ya zuwa zamanin yanzu, irin tunanin “kasashen yamma sun fi kasashen da ba su ba” ya zama makaminsu wajen ci gaba da nuna fin karfi a duniya, wato tilas ne sauran kasashen duniya su bi dukkan dokokin da suka tsara, in ba haka ba, za su dandana kudarsa.

Amma ko da gaske ne kasashen yamma sun fi wadanda ba su ba? A’a, ban yarda ba.

In mun dauki misali da batun “dimokuradiyya”, sanin kowa ne kasashen yamma su kan dauki kansu a matsayin abin koyi wajen wanzar da dimokuradiyya. Amma a hakika, dimokuradiyya ra’ayi ne da dukkan ‘yan Adam ke rungumarsa, kuma salon dimokuradiyya na kasashen yamma ba wai ainihin dimokuradiyyar da ake zance ba ne. Salon dimokuradiyya na kasashen yamma ya samo tushensa ne daga bunkasuwar tsarin jari hujja a zamanin baya, wanda ya kasance tsarin siyasa da ke kare moriyar rukunin masu jari hujja. A aikace kuma, ko a Birtaniya ko Amurka da ma sauran kasashen yamma, ‘yancin zabe na “dimokuradiyya” ya dade da kasancewa ‘yancin gungun wasu tsirarun mutane ne kawai. Ko a yau, ‘yan siyasar kasashen yamma suna wakiltar wani rukunin mutane da kuma kula da moriyarsu ne kawai, kuma suna kula da masu zabe ne kawai lokacin da za su kada kuri’a, bayan an gama, sai su bari.

Idan mun duba, kasashen yamma na fuskantar dimbin matsaloli, ciki har da gibi tsakanin masu kudi da matalauta da kabilanci da sauransu, amma hakan bai hana su yayata tsarinsu da suke ganin ya fi na sauran kasashe ba, har ma sun yi yunkurin yi wa sauran kasashe gyaran fuska. Amma hakikanan abubuwan da suka faru sun tabbatar da cewa, kasashe masu tasowa da suka yi wa gyaran fuska ma ba su kai ga tabbatar da ‘yanci da dimokuradiyya da wadata ba. A kasashen da ke kudu da Sahara, ba a kai ga fita daga kangin talauci da tashin hankali ba, a maimakon haka, su kan shiga rikici in an yi zabe. Ga kuma abin da ya faru a Afghanistan da Iraki da Libya. A ‘yan shekarun baya, wata tauraruwar kasar Amurka ta tsaya a burbushin kasar Iraki tana cewa, “duk da cewa sun rasa komai, sun samu ‘yanci.” Haka ne, watakila sun samu abun da ake kira ‘yancin a bakin kasashen yamma, amma kuma sun rasa kwanciyar hankali har da rayukansu.

Yanzu haka a fadin duniya, kasashen da ba na yamma ba suna tasowa, wadanda suke iya kokarin gano tsarin da ya dace da yanayinsu wajen tabbatar da bunkasuwarsu, kuma karin kasashe masu tasowa sun yi niyyar kin amincewa da nuna fin karfi da kashin dankali da kasashen yamma suke yi, suna kuma fatan kafa tsarin duniya da ke da karin adalci da gaskiya. Lokaci ya yi da kasashen yamma su bude idonsu su duba abubuwan da ke wakana a duniya, su yi watsi da tunaninsu na wai sun fi sauran kasashe. (Lubabatu Lei)