logo

HAUSA

Za a samu karuwar zirga-zirgar jiragen sama a kasar Sin daga lokacin zafi zuwa na kaka

2024-04-01 11:17:45 CMG Hausa

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Sin, ta ce za a samu karuwar zirga-zirgar jiragen saman fasinja, daga lokaci zafi zuwa na kaka a bana.

Hukumar ta bayyana a jiya Lahadi cewa, daga ranar 31 ga watan Maris zuwa 26 ga watan Oktoba, kamfanonin jiragen sama 188 na cikin gida da na ketare, sun shirya yin tafiye-tafiyen fasinjoji da na dakon kaya 122,000 a kowanne mako.

A bangaren zirga-zirga ta kasa da kasa, an tsara yin tafiye-tafiyen fasinjoji da na dakon kaya 17, 257 a kowanne mako, lamarin da zai hada kasar Sin da wasu kasashe 70, ciki har da kasashe 51 da suka shiga shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”.

A bangaren zirga-zirgar jiragen sama na cikin gida kuwa, kamfanonin jiragen sama 51 sun shirya yin tafiye-tafiye 101,536 a babban yankin kasar Sin a kowanne mako, karuwar kaso 2.5 idan aka kwatanta da makamacin lokacin a 2023. (Fa’iza Mustapha)