logo

HAUSA

Sojojin Isra’ila sun yi ikirarin kashe manyan jagororin Hamas biyu

2024-03-31 17:18:52 CMG Hausa

 

Rundunar sojojin Isra’ila ta ce, ta yi nasarar hallaka wasu manyan jagororin kungiyar Hamas 2, yayin ayyukan soji da take gudanarwa a asibitin Al-Shifa dake yammacin zirin Gaza.

Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar sojin Isra’ilan Avichay Adraee, ya ce a jiya Asabar, sojojinsu sun kuma hallaka wasu Falasdinawa masu dauke da makamai da dama a asibitin na Al-Shifa, ciki har da Fadi Dewik, wani babban jagoran mayakan Hamas mai lura da tattara bayanan sirri, da Zakariya Najeeb, babban jami’in Hamas mai lura da ayyukan kungiyar a hedkwatar ta dake yamma da kogin Jordan.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinawa dake zirin Gaza, ta fitar da sanarwa a jiyan, tana mai cewa tun bayan da dakarun Isra’ila suka fara kaddamar da hare-hare makwanni 2 da suka gabata a asibitin Al-Shifa, kawo yanzu akwai marasa lafiya 107 dake makale a cikin asibitin ba tare da ruwan sha, wutar lantarki ko magunguna ba. Sanarwar ta ce, rayukan wadannan marasa lafiya na cikin mummunan hadari. (Saminu Alhassan)