logo

HAUSA

Ya kamata sassan kasa da kasa su yi hadin gwiwa wajen tinkarar kalubalen bola da ake zubarwa

2024-03-31 17:19:23 CMG Hausa

Jiya Asabar 30 ga watan nan na Maris, rana ce ta bola jari ta duniya, wato “International Day of Zero Waste” a Turance. Game da wannan rana, babban sakataren MDD António Guterres ya yi jawabi ta kafar bidiyo, inda ya yi kira ga sassan kasa da kasa da su dauki matakai don tinkarar kalubalen bola da ake zubarwa.

Guterres ya bayyana cewa, nauyin sharar da ake samu daga biranen duniya a kowace shekara ya zarce ton biliyan 2, wanda ke matukar kawo babbar illa ga yanayi, da halittu, da lafiyar jikin dan Adam.

Guterres ya kalubalanci kamfanoni da su kyautata tsarin aikinsu zuwa maras gurbata muhalli, da rage yawan abubuwan kunshi, da kuma tsawaita lokacin amfani da su. Kana ya yi kira ga jama’a da su rika tunani kafin yin sayayya, da yin kokarin maimaita amfani da abubuwan da ake iya sake amfani da su. (Zainab Zhang)