logo

HAUSA

AU ta taya zababben shugaban Senegal murna

2024-03-30 17:05:43 CMG Hausa

Shugaban hukumar kula da Tarayyar Afrika AU, Moussa Faki Mahamat, ya taya Bassirou Diomaye Faye murnar lashe zaben shugaban kasar Senegal.

Wata sanarwar da AU ta fitar jiya, ta ce kungiyar na maraba da yadda dukkan bangarorin siyasa na kasar Senegal suka amince da sakamakon zaben.

Bisa sakamakon da kwamitin kidayar kuri’u na kasar Senegal ya fitar a ranar Laraba, Bassirou Faye wanda shi ne dan takarar kawancen jam’iyyun adawa, ya lashe zaben da kaso 54.28 na kuri’un da aka kada. 

A jiya Juma’a ne kuma majalisar kula da kundin tsarin mulki ta kasar Senegal ta sanar da sakamako na karshe na zaben, inda ta tabbatar da Bassirou Faye a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar a zagayen farkon da kuri’u kaso 54.28. Haka kuma, majalisar ta ce ba ta samu wani kalubale daga ‘yan takara 19 da suka fafata a zaben ba. (Fa’iza Mustapha)