logo

HAUSA

UNRWA ta bukaci Isra’ila ta bayar da damar shigar da agajin jin kai Zirin Gaza

2024-03-30 17:11:10 CMG Hausa

Philippe Lazzarini, babban kwamishinan hukumar kula da agajin jin kai da ‘yan gudun hijira Palasdinawa ta MDD (UNRWA), ya bukaci Isra’ila da ta ba jerin motocinta masu dauke da kayayyakin abinci damar shiga arewacin Gaza tare da bude karin hanyoyin mota domin saukaka kai agajin, yayin da kasashen duniya ke gargadi game da shiga matsalar yunwa a yankin.

Philippe Lazzarini, ya wallafa a shafin sada zumunta na X, rana guda bayan Kotun Duniya na MDD (ICJ) dake Hague, ta ba Isra’ila umarnin daukar dukkan matakan da suka wajaba na tabbatar da kayayyakin agaji sun isa ga al’ummar Palasdinu a Zirin Gaza.

Jami’in ya kuma yi kira ga kasashe su kara matsa lamba don ganin an aiwatar da umarnin kotun da kuma sake nazarin matakin da suka dauka game da samarwa hukumar kudade, yana mai jaddada bukatar gaggauta daukar kwararan matakai don kare yankin Gaza daga shiga matsalar yunwa.

Umarnin da kotun ICJ ta bayar a ranar Alhamis, ya biyo bayan wanda ta bayar a ranar 26 ga watan Junairu, inda ta umarci Isra’ila da ta daukidukkan matakan da suka dace na kaucewa aikata kisan kare dangi kan Palasdinawa a Gaza. (Fa’iza Mustapha)