logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamiti da zai tabbatar da ganin an fara kera motoci a kasar nan da shekaru 10 masu zuwa

2024-03-30 16:33:15 CMG Hausa

Ministar harkokin cigaban masana`antu da kasuwanci ta tarayyar Najeriya Mrs Doris Uzoka-Anite ta kaddamar da kwamiti da zai kula da aiwatar da manufofi da tsare tsaren da za su kai ga fara kera motoci da sauran ababen hawa a kasar nan da shekaru goma masu zuwa.

A jawabinta yayin kaddamar da `yan kwamitin a birnin Abuja, ministar ta ce lokaci yayi da Najeriya zata rinka samar da motoci kirar gida ga `yan kasa akan  farashi mai saukin gaske.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Ministar kasuwanci da masana`antun ta tarayyar Najeriya ta ce `yan Najeriya na fuskantar kalubale mai yawan gaske a fannin sufuri, a saboda haka ya zama wajibi a samar masu da mafita ta hanyar kera ababen hawan da suka dace da su .

Ta ce sakamakon karuwar farashin kudaden musaya da kudaden haraji na fito, sama da kaso 50 na al`ummar kasar ba sa iya mallakar ababen hawa, sannan kuma samfurin ababen hawan musamman motoci da ake shigowa da su daga kasashen ketare ba su dace da yanayin titunan kasar ba.

Mrs Doris Uzoka tace tana da yakinin wa`adin shekaru goma da gwamanti ta diba domin cimma wannan buri zai baiwa Najeriya damar kasancewa daya daga cikin kasashen da suka yi fice wajen kera motoci da sauran ababen hawa.

“Najeriya tana da arzikin da za ta iya samar da ababen hawanta domin kuwa muna da albarkatu, muna da fasahar kere kere, muna da kasuwa sannan kuma yanzu muna da tsarin da zai taimake mu wajen samar da ababen hawan mu”

Ababen hawan da za a rinka kerawa sun hada da kananan motocin hawa da Babura da motocin dakon kaya da sauran motocin da kamfanonin gine gine ke amfani da su.

An zabo `yan kwamitin ne daga hukumar lura da harkokin fasahar kere-kere ta kasar, ma`aikatar kudi da ma`aikatar masana`antu da hukumar kwastam da kungiyoyin masu masana`antu ta kasa da kuma sauran masu ruwa da tsaki.(Garba Abdullahi Bagwai)