logo

HAUSA

Kocin wasan damben Boxing daga Cuba na taka rawar gani wajen horas da kwararrun ‘yan wasa a Xinjiang

2024-03-29 14:58:38 CGTN HAUSA

A filin wasan damben boxing da aka gina can kasan tsaunin Tianshan, kocin horas da wasan daben boxing dan asalin kasar Cuba Dagoberto Capote, na matsawa wurare daban daban cikin sauri, yana kai bugu da gaggawa ga dan wasan da yake horaswa dan asalin yankin Xinjiang.

Duk da ya kai shekaru 56 a duniya, koci Capote na cike da kuzari da sha’awar wasan da yake koyarwa, yana motsawa da kyau tamkar matashin dan dambe dake shiga da’irar wasan a karon farko.

Capote na cike da karsashi, yana furta jimloli irin su "jiayou" dake nufin kara kaimi da harshen Sinanci, da kalmar "champion" da harshen faransanci, inda yake ta karawa ‘yan wasan sa kwarin gwiwar cimma nasara a dukkanin fannonin samun horon su. Bisa salon sa mai jan hakalin dalibansa, darasin horaswar na kara karsashi, da samar da yanayi mai nishadantarwa.

Da yake tsokaci kan irin yadda yake cike da karsashi yayin da yake koyar da ‘yan wasansa, Capote ya ce "Kuzari a cikin jinin dukkanin ‘yan Cuba yake, kusan hakan gado ne. Dole ne koci mai kwarewa ya zama yana da ilimin wasan, amma bayan hakan wajibi ne ya san yadda zai ja hankalin ‘yan wasansa su kasance cikin nishadi a duk tsawon horo".

Yayin da yake tsaka da wasan dambe, Capote ya kasance dan wasa mai hazaka, ya kuma lashe wasanni daban daban a matakin kasa. Bayan ya yi ritaya daga Boxing, sai ya zama mai horas da ‘yan wasa saboda sha’awar wasan da yake yi, inda ya ci gaba da koyar da ilimin kwarewa da ya samu a Cuba, da Venezuela, a yanzu kuma ya dawo Xinjiang na kasar Sin.

A watan Yunin shekarar da ta gabata, bayan gamsuwa da yanayin aiki da suka samu, Capote da abokin horaswarsa Luisbey Sanchez, sun tsallaka teku zuwa Xinjiang inda suka karbi aikin horas da manya, da matasan ‘yan wasan dambe dake jihar.

Wasan damben Boxing ya samu karbuwa matuka a yankin, inda matasa daga kabilun Kazakh, da Uygur, da sauran su ke shiga a dama da su a wannan wasa. Cikin shekarun da suka gabata, Xinjiang ta samar da ‘yan damben Boxing masu hazaka da suka hada da Mehmet Tursun Chong, da Tohtarbek Tanglathan, wadanda suka cimma manyan nasarori a gasannin kasa da kasa.

Da isar sa Xinjiang, Capote ya bayyana cewa, ya ji nauyi babba a wuyansa sakamakon tarihin da yankin ke da shi a wasan boxing. Don haka sai ya fara da dunkule sabon salon horaswa, da dabaru daban daban na karfafa sassan da ‘yan wasan da yake horaswa ke da rauni.

Koci Capote ya ce "’Yan wasan boxing din wannan yanki suna da yanayi na karfin jiki, amma ina mayar da hankali ga inganta dabarun su na wasan ta yadda za su kara samun kwarewa a dukkanin fannoni".

Bayan duk zangon horaswa, Capote na baiwa ‘yan wasansa alawa don karfafa gwiwar su, da jan hankalin su wajen ci gaba da kara kwazo.

Ba tare da bata lokaci ba kuwa sai kokarinsa ya haifar da nasara, inda jihar Xinjiang ta lashe lambobin zinari 3, da azurfa daya da tagulla 1, a gasar kasa da ta gudana a watan Disamban bara, wanda hakan ya tabbatar da ci gaban da aka samu a yankin.

Kasancewar ya yi matukar nisa da gida, wasu lokuta Capote kan yi kewar gida da iyalinsa. Game da hakan, ya ce ya yi kokarin sabawa da rayuwar Xinjiang, daga jure yanayin hunturu zuwa nau’o’in abinci, wadanda suka yi matukar sabawa wadanda ya saba da su a gida, Capote na kallon hakan a matsayin wani sabon babi a rayuwarsa. Yana yawan daukar hotuna a duk lokacin da yake tafiye tafiye a cikin kasar Sin, da nufin nunawa iyalansa abubuwan da ya gani yayin da ya koma gida.

Ya ce sauran ma’aikata da suke taya shi aikin horas da ‘yan wasa sun zama iyali na biyu gare shi. Bayan shafe kusan shekara guda tare da su, a yanzu koci Capote yana daukar dalibansa a matsayin ‘ya’yansa.

A nasu bangaren, su ma ‘yan wasansa na daukar sa da muhimmancin gaske, a wani lokaci da ya gamu da tsananin ciwon ciki da dare, sun yi gaggawar tallafa masa, sa’an nan suka samar masa da abinci. Daya daga cikin su mai suna Alikut Qahar, ya ce "Koci Capote na cike da karsashi yayin bayar da horo, da ma a harkokin rayuwarsa baki daya. Ina godewa tallafinsa gare ni".

Wasu lokuta Capote kan gamu da kadaici, kuma game da hakan ya ce "Kadaici ya zama dole, amma na zo Xinjiang ne da wani buri. Tun da kowa ya amince da ni, dole na yi duk abun da zan iya domin ganin damben boxing a Xinjiang ya samu manyan nasarori".

A shekarun baya bayan nan, masu horas da ‘yan wasan dambe daga Cuba kamar Capote, sun samu damammaki da yawa na samun ci gaban sana’a a kasar Sin. Baya ga tawagar kasa, akwai kuma lardin Henan, da Shandong da Anhui, wadanda su ma suka ci gajiya daga horaswar ‘yan Cuba.

Sau da dama Capote kan gamu da tsofaffin abokai a wuraren gudanar da gasanni daban daban. Matakin da yake dawo masa da tunanin lokutan baya, amma da zarar ‘yan wasansu sun shiga filin dambe, sai kowa ya shiga aiki tukuru.

Game da hakan, Capote ya ce "Da zarar mun shiga da’irar dambe sun zama abokan hamayya. Amma a waje, mu abokai ne kamar kullum. Ina fatan zuwan mu zai daga matsayin dambe a kasar Sin zuwa matakin koli. Idan zai yiwu ina fatan zama a Xinjiang don horas da karin ‘yan wasan dambe na lokaci mai tsawo".

Caote ya bayyana hakan tare da imanin cewa, wasan damben boxing a kasar Sin zai ci gaba da bunkasa cikin sauri.