logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta kafa sansanin soji a yankin tafkin Chadi

2024-03-28 11:32:29 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa, tana nan tana shirin samar da sansanin soji na musamman a yankin tafkin Chadi da zummar kyautata sha’anin tsaro a yankin.

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ne ya bayyana hakan lokacin da ya gana da manema labarai jim kadan da kammala tattaunawa da shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa dake birnin Abuja, ya ce, samar da sansanin zai baiwa manoman yankin kwarin gwiwar komawa gonakinsu.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce, daga cikin manufar samar da sansanin sojin sun hada da samar da cikakkiyar dama ga manoma wajen noman abinci a yankin, wanda rashin tsaro a baya ya hana.

Ya ce, gwamnati tana kokari wajen farfado da shirin noman rani na yankin kudancin Chadi da kuma na Yauri dake arewacin Borno sakamakon ingantuwar tsaro a jihar ta Borno, yin hakan kamar yadda ya ce zai taimaka sosai wajen wadatuwar abinci a Najeriya.

Gwamnan na jihar Borno ha’ila yau ya ce, sun tattauna da shugaban kasa a game da batun debo ’yan Najeriya dake gudun hijira a kasashen Kamaru da Chadi da kuma Jamhuriyyar Nijar wanda a baya aka fara kwaso su amma kuma aka dakatar saboda yanayin damuna da kuma babban zaben kasar da ya gabata.

“Shugaban kasa ya ba ni tabbacin cewa, gwamnatin Najeriya za ta koma aikin debo mutanen nan ba da jimawa ba.”

Gwamnan ya sanar da cewa, ya zuwa yanzu, sama da mutane ’yan gudun hijira dubu 100 ne aka kwaso zuwa Borno cikin shekaru 6 zuwa 7 da suka gabata daga  kasashe makwafta. (Garba Abdullahi Bagwai)