logo

HAUSA

Sin ta zamo ta daya a yawan jarin waje da ake zubawa a Tanzania

2024-03-28 09:58:52 CMG Hausa

Babban sakatare a ofishin tsare-tsare da bunkasa juba jari na kasar Tanzania Tausi Kida, ya ce kasar Sin ce kan gaba a fannin zuba jarin waje na kai tsaye ko FDI a kasar, wanda hakan ya taimaka wajen bunkasa ci gaban Tanzania.

Mista Kida, ya bayyana hakan ne a jiya Laraba a birnin Dar es Salaam, yayin kammala taron tattaunawa na yini guda na zuba jari tsakanin Sin da Tanzania, da taron habaka harkokin cinikayya da zuba jari na Sin (Jinhua) da Tanzania.

A cewar jami’in, daga watan Janairun shekarar 2021 zuwa watan Disamban 2023, cibiyar zuba jari ta Tanzania, ta yi rajistar ayyukan zuba jari daga Sin wadanda yawansu ya kai 256, kana kimarsu ta kai kimanin dala biliyan 2.5. Kaza lika, sassan da ayyukan suka shafa sun hada da na samar da hajoji, da gine-ginen kasuwanci, da noma, da sufuri da kuma fannonin bayar da hidima.  (Saminu Alhassan)