logo

HAUSA

Bassirou Diomaye Faye ya lashe zaben shugaban kasar Senegal

2024-03-28 09:47:06 CMG Hausa

Hukumar kidayar kuri’un da aka kada yayin babban zaben kasar Senegal, ta ce dan takarar gamayyar ’yan adawa Bassirou Diomaye Faye, ya lashe babban zaben kasar da kuri’u mafiya rinjaye.

Yayin taron manema labarai da aka gudanar a jiya Laraba a Dakar, fadar mulkin kasar, shugaban hukumar Amady Diouf ya ce sakamakon da aka tattara ya nuna mista Faye ya samu jimillar kuri’u 2,434,751, wato kaso 54.28 bisa dari na jimillar kuri’un da aka kada, yayin da dan takara mai biye masa baya daga gamayyar jam’iyyu masu mulki Amadou Ba, ya samu kaso 35.79 bisa dari na kuri’un da aka kada.

Amady Diouf ya kara da cewa, kaso 61.30 bisa dari na ’yan kasar da suka cancanci zabe ne suka kada kuri’unsu a babban zaben kasar na wannan karo.   (Saminu Alhassan)