Me ke jawo hankalin kamfanonin kasa da kasa zuwa Sin?
2024-03-28 17:12:08 CMG Hausa
A baya bayan nan, manyan kamfanonin kasa da kasa suna kara shigowa kasar Sin domin gudanar da hada-hadar kasuwanci, da kaddamar da sabbin hajoji, da gudanar da baje koli da dai sauransu. Kamfanonin waje na da yakinin cewa, akwai tarin damammaki na cin gajiya daga babbar kasuwar kasar Sin, don haka suke ta kara fadada jarin da suke zubawa a kasuwannin kasar.
Ko shakka babu, wannan tagomashi bai zo da mamaki ba, duba da wasu matakai masu ma’ana da mahukuntan Sin suke dauka domin ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar.
Alkaluman baya bayan nan na hukumar kididdiga ta kasar Sin, sun nuna yadda cikin watanni 2 na farkon shekarar bana, tattalin arzikin kasar ya fadada, tare da samun karin inganci. Kuma shaidu na zahiri sun nuna tattalin arzikin na Sin na da ginshiki mai karfi dake daidaita shi, baya ga babbar dama ta kara bunkasarsa a nan gaba.
Cikin manyan manufofi da kasar Sin ta kaddamar masu ingiza wannan nasara, akwai managartan matakan daidaita tattalin arziki, da ingiza bude kofa, da samar da kyakkyawan yanayin kasuwa ga masu zuba jari daga waje.
Wasu alkaluma na ma’aikatar cinikayyar kasar Sin sun nuna a watanni 2 na farkon shekarar nan ta 2024, adadin sabbin kamfanoni masu jarin waje da aka yiwa rajista a kasar Sin sun kai 7,160, wanda hakan ya nuna karuwar kaso 34.9 bisa dari na irin wadannan kamfanoni a shekara guda. Bugu da kari, darajar yawan jarin waje na kai tsaye da aka yi amfani da shi a babban yankin kasar Sin ya kai kudin Sin yuan biliyan 215.09, wato kimanin dala biliyan 30.29, inda aka yi amfani da yuan biliyan 28.27 a sashen raya manyan fasahohi kere-kere.
Abu ne mai faranta rai ga sassa masu zuba jarin waje, ganin yadda kasar Sin ta matsa gaba daga matakin samar da ci gaba da aka saba gani, zuwa matakin bunkasa ci gaba mai inganci, wanda ke kunshe da tarin damammaki na rasa kai, da kuma cin gajiya ga sauran sassa na kasa da kasa.
A shekarar bana, rahoton ayyukan gwamnatin kasar Sin, ya gabatar da shawarar kawar da shingaye dake shafar damammakin zuba jarin waje a sassan kere-kere, da rage wasu shingayen a fannonin bayar da hidima, kamar na fasahohin sadarwa da kiwon lafiya.
Idan mun yi hangen nesa, za mu ga cewa kasar Sin na da zarafi na ci gaba da dunkulewa tare da sauran sassan duniya, ta hanyoyinta na bude kofa a matsayin koli. Ko shakka babu, a nan gaba duniya za ta kara yin hadin gwiwa da kasar Sin bisa tafarkinta na samar da ci gaba, kuma Sin din za ta ci gaba da fadada damammakinta na hadin gwiwar cimma moriyar juna, yayin da a daya hannun za ta ci gaba da zama jigon wanzar da daidaito, a fannin bunkasa ci gaban duniya baki daya. (Saminu Alhassan)