logo

HAUSA

Ministan cikin gida na Nijar ya tattauna tare da jakadar Amurka dake Nijar

2024-03-28 18:31:58 CMG Hausa

A ranar jiya Laraba 27 ga watan Maris din shekarar 2024, ministan cikin gida, janar Mohamed Toumba ya gana da jakadiyar Amurka da ke Nijar madam Kathleeen Fitz Gibbon a ofishin ma’aikatar da ke birnin Yamai.

Daga birnin Yamai din abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

A yayin wannan ganawa ta kud da kud, batutuwa da dama ne aka tattauna da suka shafi huldar dangantaka tsakanin kasar Amurka da kasar Nijar, da kuma suka fi janyo hankalin manyan jami’an biyu.

Dalilin haka ne, a lokacin wannan ganawa madam Kathleen Fitz Gibbon, jakadar kasar Amurka a Nijar, ta bayyana cewa kasarta ta amince da matakin sabbin hukumomin kwamitin ceton kasa na CNSP na yin allawadai da babbar murya da yarjejeniyar soja da ta hada kasar Nijar da kasar Amurka a wannan muhimmin fannin batun tsaro.

Haka kuma ta tabbatar da cewa, kasarta za ta je ta dawo tare da wani sabon shiri da za’a tattaunawa kansa tare da bangaren Nijar domin tsaida manufofi tare kan sharudan da suka shafi janyewar jojojin Amurka da ke cikin kasar Nijar.

A wani fanni na daban, jami’ar diplomasiyyar kasar Amurka ta dauki alwashi tare da jaddada niyyar kasarta wajen kasancewa har kullum tare da kasar Nijar, wannan kuma ta hanyar rakiyar ayyukan ci gaban al’umma da tuni kungiyar USAID ta kasar Amurka take cikin yi a Nijar.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar.