logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a kwantar da halin a gabashin Kongo Kinshasa

2024-03-28 11:24:59 CGTN HAUSA

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi kira ga bangarori masu ruwa da tsaki a Kongo Kinshasa, da su yi iyakacin kokarin kwantar da hali game da yanayin da ake ciki a gabashin kasar.

Dai Bing wanda ya bayyana hakan cikin jawabinsa a zaman kwamitin sulhun MDD kan batun Kongo Kinshasa da ya gudana a jiya Laraba, ya ce a kwanan baya, halin da ake ciki a gabashin kasar ya kara tsananta, musamman ma ganin yadda rikici ya barke a kan iyaka, lamarin da ya yi sanadin asarar rayukan fararen hula, kana wasu kuma suka tserewa gidajensu.

Ya ce hakan abun damuwa ne, kuma bai kamata a bar hakan ya dore ba. Sin na kira ga kungiyoyin fafutuka, ciki har da M23, da su tsagaita bude wuta, da janye jikinsu daga wuraren da suka mamaye. Kaza lika, Sin na kira ga bangarorin da su kai zuciya nesa, su daidaita bambancin ra’ayi ta hanyar yin shawarwari, ta yadda za su yi iyakacin kokarin kwantar da hankali a yankin.

Ban da wannan kuma, a cewar sa tun daga shekarar 2003, Sin ta tura sojoji injiniyoyi, da tawagogin ba da jiyya, da kiyaye zaman lafiya har sau 27 zuwa kasar. Dai ya ce tawagogin sun sauke nauyin dake wuyansu yadda ya kamata duk da mawuyancin hali da suka fuskanta. Har ila yau, Sin tana fatan yin hadin gwiwa da kasashen duniya, wajen taka rawar gani a fannin shimfida zaman lafiya mai ingiza ci gaban kasar. (Amina Xu)