logo

HAUSA

An amince da sabon kundin tsarin mulkin kasa a Togo

2024-03-27 11:37:38 CMG Hausa

Majalissar dokokin kasar Togo, ta amince da sauyin da aka yiwa kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya tanadi mayar da kasar kan tsarin mulkin falamantare daga tsarin shugaba mai cikakken iko da kasar ke kai.

Wata sanarwa da fadar gwamnatin kasar ta fitar a jiya Talata, ta ce a daren ranar Litinin, majalissar dokokin kasar Togon ta amince da wannan sauyi, bayan samun kuri’un amincewa 89, cikin jimillar kuri’u 91 da aka kada kan kudurin.

Sanarwar ta kara da cewa, daga yanzu majalissar dokoki ce za ta rika zabar shugaban janhuriyar kasar yayin zamanta, kuma shugaban zai yi zango daya na shekaru 6 ne kacal.

Kafin wannan sauyi, al’ummar Togo ne ke zabar shugaban kasa ta zaben gama gari, inda zababben shugaban kasar ke da ikon rike ragamar shugabanci na tsawon shekaru 5, da kuma damar yin tazarce sau daya.

Rubutaccen kundin tsarin mulkin kasar da aka amincewa, ya kira wani sabon mukamin da aka kafa da "shugaban majalissar ministoci", mai ikon jagorancin harkokin gwamnati a tsawon shekaru 6 karo daya, kuma wanda majalissar dokokin kasar ke da ikon bibiyar ayyukan sa. (Saminu Alhassan)