logo

HAUSA

Amurka ba ta nuna sahihanci kan batun tsagaita bude wuta a yankin Gaza

2024-03-27 15:15:45 CGTN HAUSA

 

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Geng Shuang, ya yi jawabi a gun taron kwamitin sulhu na majalisar kan batun Palasdinu da Isr’aila, inda ya dasa ayar tambaya dangane da matsayin da Amurka ke dauka kan batun tsagaita bude wuta a yankin Gaza, duba da yadda ta gaza nuna sahihanci kan hakan.

Ya kuma kara da cewa, kwamitin sulhun ya zartas da kuduri mai lamba 2728 a Litinin din da ta gabata, wanda ya bukaci dakatar da bude wuta a watan Ramadam a yankin, kuma mambobin kwamitin 14 ciki har da Sin sun kada kuri’un amince da shi, inda Amurka ta ki jefa kuri’arta. Bayan Amurka ta gurgunta matakai masu amfani da kwamitin yake dauka sau da dama, a wannan karo ta ki jefa kuri'a, wanda hakan tamkar ci gaba ne ta samu, sai dai kuma matakin da ta dauka a hakika ya sabawa hakan, shi ya sa ake dasa ayar tambaya kan matakin siyasarta da sahihancinta.

Geng Shuang ya kuma jaddada cewa, Sin na kalubalantar Isra’ila da ta nace ga kudurin kwamitin, ta dakatar da bude wuta a yankin Gaza, da daina cin zarafin fararen hular Gaza. Kaza lika Sin na bukatar Amurka da ta dauki matakan da suka dace, na yin tasiri mai yakini ga Isra’ila, don ta tabbatar da nasarar kudurin bisa matakin da take iya dauka. (Amina Xu)