Mene ne kare hakkin dan Adam ke nufi, Yaya za mu kare hakkin dan Adam?
2024-03-27 08:24:09 CMG Hausa
Don mutunta hakkin dan Adam ana amfani da matakai da dama da kuma yin aiki tare don neman mafita ga matsalolin duniya. Hakan ya sanya aka samar da dokokin hakkin dan Adam na kasa da kasa da sauran dokoki masu nasaba da kare hakkin dan Adam, wadanda suka kasance ginshikan alkawuran kasashe na duniya.
Amma a yau, kasashe da suka rubuta kuma suka amince da wadannan dokoki suna ci gaba da kalubalantar tushen wadannan dokokin, ko kuma suna kara neman lalata su, ko ma rusa wadannan ka'idodin hakkin dan Adam. Sakamakon hakan shi ne rashin zama lafiya da duniya ta tsunduma ciki. Babu wata zama da za a yi a Majalisa Dinkin Duniya ba a tabo batun kare hakkin dan Adam ba, sai dai kiran ba ya yin tasiri musamman ma idan daga kasashe masu tasowa ne. Hakan ya sanya a yayin taro karo na 55 na kwamitin kare hakkin bil'Adama na MDD, Chen Xu wato zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya yi tir da yadda ake siyasantar da batutuwan da suka shafi hakkin dan Adam a cikin wata sanarwar da aka fitar a madadin kungiyar abokai kan bunkasa hakkin dan Adam ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa.
Yanayin siyasa da rashin jituwa yana kara ta'azzara a kwamitin kare hakkin bil'Adama na MDD, wanda ya yi hannun riga da manufar kwamiti din ta asali, kuma ya saba wa ka'idojin dunkulewar kasa da kasa, da nuna son kai. Mun ga a lokuta da dama yadda akan kai ruwa rana a MDD game da batutuwa da suka shafi kare hakkin dan Adam a wasu kasashen duniya musamman Gabas ta tsakiya.
Bari mu tabo batun Jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta kasar Sin wanda a lokuta da dama kasashen yammacin duniya ke ma kasar Sin katsalandan da ikirarin cewa ana kutantawa mazauna yankin, duk da cewa rahotannin daga jam’ian gwamnatin kasashe da dama wadanda su kai ziyarar gani da ido a yankin sun wanke kasar Sin game da wadannan tuhume-tuhumen tare da shelanta irin ci gaba da ake samu a yankin. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Mohammed Yahaya)