logo

HAUSA

Wani rikici ya barke a tsakanin wasu al’umomi a jihar Filato

2024-03-27 09:20:07 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Filato dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta  tabbatar da mutuwar wasu mutane 6, sannan kuma wasu 30 suka samu munanan raunika bayan da gidaje sama da 40 suka kone sakamakon rikici da ya barke tsakanin wasu al’umomi dake kauyukan kananan hukumomin Mikang da kuma Langtang a jihar.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai a game da al’amarin, kwamashinan yada labaran jihar Hon Musa Ashome ya bayyana rikicin a matsayin babban abun takaici.

Daga tarayyar Najeriya Wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Kwamshinan yada labaran na jihar ta Filato ya ce, rikicin wanda ya samo asali daga takaddama a kan filaye a tsakanin al’umomin biyu, haka kuma ya yi sanadiyar kone rumbunar ajiyar kayan abinci da dama.

Ya ce da jimawa al’umomin suna zaune lafiya da juna, har ma ana samun auratayya a tsakaninsu, amma kuma rikicin filayen da ba za a iya noma buhu 6 na shinkafa ba ya yi sanadin asarar wadannan rayuka da kuma kaddarorin masu dimbin yawa.

Mr. Musa Ashomes ya ce, duk da dai sau tari a wasu lokuta ana samun rashin jituwa tsakanin al’umomin da suka hada iyaka da juna a Najeriya, amma ba a iya warware irin wannan matsala ta hanyar fada da juna.

“A duk lokacin da kuka sami sabani da juna, bai dace ba a yi amfani da makami wajen neman masalaha, a don haka a matsayinmu na gwamnati  mun yi alawadai da abin da ya faru na rashin tunani kuma abin takaici, domin kuwa lamari ne da za a iya warware shi cikin ruwan sanyi.”

Kwamashinan yada labaran na jihar Filato ya tabbatar da cewa yanzu zaman lafiya ya dawo a yankunan da rikicin ya afku bayan da aka sami karin jami’an tsaro, inda ya yaba matuka da kokarin kwamashinan ’yan sandan jihar da kuma sauran hukumomin tsaro. (Garba Abdullahi Bagwai)