logo

HAUSA

An yi tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaba Abdrouhamane Tiani da shugaba Vladmir Putin na kasar Rasha

2024-03-27 08:59:50 CMG Hausa

A ranar jiya da misalin karfe 9 na safe na ranar Talata 26 ga watan Maris din shekarar 2024, shugaban mulki soja a Nijar, kuma shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP, Abdrouhamane Tiani ya tattauna ta wayar tarho tare da takwaransa na kasar Rasha Vladmir Putin.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Ita dai wannan tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugabannin kasashen biyu ta biyo bayan wata wasikar taya murna da shugaban kasar Nijar ya aika wa takwaransa na kasar Rasha Vladmir Putin bayan ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a makon da ya gabata.

Kuma tattaunawar ta maida hankali kan batutuwan dake jan hankalin kasashen biyu, da kuma batutuwan dake shafar kasa da kasa. Shugabannin biyu sun kuma tattauna kan muhimman batutuwa da suka hada da sakon ta’aziya da sakon taya murna, da kuma godiya bisa ga gudunmawar da kasar Rasha take kawo wa kasar Nijar game da kokowar neman ’yancin gashin kanta, da wajabcin karfafa huldar dangantaka ta fuskar tsaro tare da kasar Rasha, domin fuskantar barazanar tsaro ta yanzu, da ingiza musanyar kwarewa da cin moriyar juna tare da kasar Rasha, domin amfanin kasashen biyu.

Ku rike cewa, wannan tattaunawa ta wayar tarho ta gudana a fadar shugaban kasa dake birnin Yamai, a gaban idon faraministan gwamnatin rikon kwarya Ali Mahamane Lamine Zeine, da janar Salifou Mody, ministan tsaron kasa, da birgadiya janar Mohamed Toumba, ministan cikin gida, da ministan harkokin wajen kasar Nijar, Bakary Yaou Sangare da kuma sauran mambobin kwamitin ceton kasa na CNSP da kuma na gwamnatin rikon kwarya.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.