logo

HAUSA

Yadda aka yi jimamin wadanda suka halaka a harin ta'addanci a kasar Rasha

2024-03-26 17:16:27 CMG Hausa

Yadda al’ummar kasar Rasha ke jajantawa wadanda suka rasa rayukansu a harin ta’addanci da aka kai wani zauren kide-kide da ke kusa da birnin Moscow. Bayan da shugaban kasar ta Rasha Vladimir Putin ya bayyana ranar 24 ga wata a matsayin ranar jimami na kasar, an gudanar da harkokin jimamin wadanda suka halaka a harin a sassa daban daban na kasar.