logo

HAUSA

Sinawa 5 na daga cikin mutane 6 da harin ta’addanci a arewa maso yammacin Pakistan ya rutsa da su

2024-03-26 21:46:08 CMG Hausa

Wani harin ta’addanci da aka kai lardin Khyber Pakhtunkhwa dake arewa maso yammacin Pakistan a yau Talata, ya yi sanadin mutuwar Sinawa 5 da dan kasar Pakistan 1.

Ofishin jakandanci kasar Sin dake Pakistan ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce lamarin ya auku da misalin karfe 1 na rana, a lokacin da wasu ‘yan ta’addan suka kai hari kan motoci mallakar ma’aikatan dake aikin ginin madatsar ruwa ta Dasu, wanda aka ba kamfanin kasar Sin kwangilar  ginawa.

Wata sanarwa daga ofishin jakadancin Sin a Pakistan, ta ruwaito ofishin da sauran kananan ofisoshinta dake fadin kasar, na yin Allah wadai da harin na ta’addanci, inda suka jajantawa iyalan wadanda harin ya rutsa da su a kasashen biyu. Sun kuma bukaci kasar Pakistan ta aiwatar da cikakken bincike game da lamarin.

Shi ma shugaban kasar Pakistan Asif Ali Zardari ya fitar da wata sanarwa a yau Talata, inda a cikinta ya yi tir da harin, yana mai cewa masu adawa da kasarsa, ba za su taba nasara ba wajen illata abotar dake tsakaninta da kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)