logo

HAUSA

Malaman BUK sun yaba da kokarin da ‘yan China suke yi wajen tallata harshen Hausa

2024-03-26 16:01:03 CMG Hausa

Farfesa Yakubu Magaji Azare, da Farfesa Aliyu Mu’azu, malamai ne a jami’ar gwamnatin tarayyar Najeriya ta Bayero dake Kano, wadanda suka shigo birnin Beijing na kasar Sin a karshen makon da ya gabata, don halartar taron karawa juna sani na kasa da kasa, kan nazarin harsuna gami da al’adun Afirka na shekara ta 2024.

A zantawarsu da Murtala Zhang, malaman sun bayyana ra’ayoyinsu kan kokarin da daliban kasar Sin suke yi na koyon harshen Hausa da nazarin al’adun Hausawa, gami da yadda za’a yi don shawo kan kalubalen da harshen Hausa ke fuskanta. Kaza lika sun bayar da wasu shawarwari ga dalibai, gami da ‘yan jaridun kafafen yada labarai masu amfani da harshen Hausa don kara inganta harshen na Hausa. (Murtala Zhang)