logo

HAUSA

Kwamitin tsaron MDD ya amince da kudurin neman tsagaita wuta a Gaza albarkacin watan Ramadan

2024-03-26 10:07:08 CMG Hausa

Kwamitin tsaron MDD ya amince da kuduri mai lamba 2728, mai kunshe da neman a tsagaita bude wuta a Gaza albarkacin watan azumin Ramadan mai alfarma.

Kudurin dai ya samu kuri’un amincewa 14 cikin jimillar kuri’u 15. Kafin wannan kuduri, Amurka ta hau kujerar na ki kan makamantansa 3 da aka gabatar a baya, kana a jiya Litinin ta ki jefa kuri’a game da sabon kudurin da aka gabatar.

Sabon kudirin shi ne na farko da kwamitin tsaron MDDr ya amincewa, wanda ya bukaci dakatar da bude wuta a Gaza, tun bayan sake barkewar tashin hankali tsakanin Isra’ila da Falasdinawa a ranar 7 ga watan Oktoban 2023. Barkewar tashin hankali a wannan karo ya haifar da kisan Falasdinawa 32,333, baya ga kusan 75,000 da suka jikkata, kamar dai yadda ma’aikatar lafiya ta yankin Gaza ta tabbatar.

A cewar wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, kudurin mai lamba 2728, ya bukaci dukkanin sassa masu ruwa da tsaki da su dakatar da bude wuta nan take a Gaza a duk tsawon watan nan na Ramadan, matakin da ake fatan zai kai ga wanzuwar tsagaita wuta baki daya. Zhang Jun ya kuma yi kira da a aiwatar da kudurin yadda ya kamata.  (Saminu Alhassan)