logo

HAUSA

Fadar White House: Janyewar Amurka daga kudurin tsagaita bude wuta a Gaza ba ya nufin sauya manufar kasar

2024-03-26 10:25:52 CMG Hausa

Kakakin kwamitin tsaron fadar White House John Kirby, ya bayyana a yayin gabatar da takaitaccen bayani a jiya Litinin cewa, “A yau Amurka ta janye jiki daga kudurin baya bayan nan na tsagaita bude wuta a zirin Gaza wanda aka gabatar yayin zaman kwamitin tsaron MDD, sai dai hakan ba ya nufin sauya manufar kasar”.

Kirby ya bayyana cewa, Amurka ta nuna goyon baya ga sakin mutanen da aka tsare, karkashin kudurin na tsagaita bude wuta, amma sashen karshe bai dora muhimmanci ga yin Allah wadai da Hamas ba, don haka Amurka ta ki nuna goyon bayan kudurin gaba daya, maimakon haka ta janye jiki daga kada kuri’a kan kudurin.

Mista Kirby ya kara da cewa, a jiyan ministan tsaron kasar Isra’ila Yoav Gallant ya ziyarci Amurka, kuma bangaren Amurka zai bayyana wa Gallant cewa, Amurka za ta ci gaba da goyon bayan Isra’ila wajen yaki da Hamas. (Safiyah Ma)