Jakadan Sin dake Nijar ya gana da firaministan gwamnatin wucin gadin kasar
2024-03-26 10:43:25 CGTN HAUSA
Jakadan Sin dake jamhuriyar Nijar Jiang Feng, ya gana da firaministan gwamnatin wucin gadin kasar Ali Mahamane Lamine Zeine a jiya Litinin, inda suka yi musanyar ra’ayi kan hadin gwiwa a fannin man fetur.
Jiang Feng ya ce bangarorin biyu sun samu ci gaba mai armashi a cikin shekaru 20 da suka gabata a wannan bangare. Ya ce yankin hakar mai na Agadem kyakkyawan misali ne na hadin gwiwar kasashen biyu, inda ya zuwa yanzu ake aikin hakar danyen man fetur a mataki na 2, domin jigilarsa zuwa kasuwar kasashen duniya ta bututu mafi tsawo a nahiyar Afrika, wanda kasashen biyu suka yi hadin gwiwar shimfidawa. Jakadan ya ce Sin za ta ci gaba da nacewa ga matsayin nuna sahihanci da gaskiya, da kara hadin kai don more dabaru da basirar bunkasuwa tare da Nijar.
A nasa bangare, firaministan Zeine cewa ya yi Sin kawar Nijar ce, kuma Nijar na sa ran samun ci gaban hadin kansu. Ya ce filin hakar danyen mai na Agadem, na kunshe da kyakkyawan fatan gwamnatin kasar, da jama’arta, wajen samun ikon mulkin kai da bunkasuwa. Daga nan sai ya yi fatan aikin jigilar danyen man fetur daga Nijar zuwa ketare, zai gaggauta bunkasuwar tattalin arziki da inganta rayuwar al’ummar kasar, ta yadda karin fararen hula za su amfani ci gaban hadin kan kasashen biyu. (Amina Xu)