logo

HAUSA

Faransa ta daga matsayin gargadin ta'addanci bayan harin Moscow

2024-03-25 11:03:21 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Faransa ta yanke shawarar daga matsayin gargadin aukuwar ta'addanci zuwa matakin koli, a wani mataki na dakile barazanar da kasar ke fuskanta, bayan mummunan harin ta'addanci da ya auku a birnin Moscow na kasar Rasha a ranar Juma'a.

Cikin wani sakon X da ya wallafa, firaministan Faransa Gabriel Attal, ya ce a daren jiya Lahadi shugaban kasar Emmanuel Macron, ya kira taron tsaro a fadar gwamnati ta "Elysee Palace". Mista Attal ya ce "la'akari da ikirarin kungiyar ISIS da kaddamar da harin, da barazanar hakan ga kasar mu, mun yanke shawarar daga mizanin gargadi zuwa matakin ko ta kwana".

A kalla mutane 137 ne suka mutu a birnin Moscow, sakamakon harin ta'addancin da aka kaddamar a wani babban dakin taron jama'a, yayin da ake taron kade-kade da wake-wake, a ranar Juma'ar da ta gabata.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ayyana jiya Lahadi a matsayin ranar makoki ta kasa, cikin jawabin da ya gabatar ta kafar talabijin. (Saminu Alhassan)