logo

HAUSA

Hukumar kwastam a tarayyar Najeriya ta yi gwanjon katan-katan na Ashana ’yar kasar waje a jihar Katsina

2024-03-25 09:09:37 CMG Hausa

Hukumar kwastam a tarayyar Najeriya ta yi gwanjon katan dubu 3,522 na Ashana ’yan kasar waje a jihar Katsina dake arewacin kasar.

A lokacin da yake jagorantar sayar da kayan a birnin Katsina, babban kwamandan hukumar mai lura da shiyyar arewa maso yamma Mr. Kola Oladeji, ya ce, an sayar da kowanne katan a kan Naira dubu 5 maimakon naira dubu 13.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Kwantrolan hukumar ya ce, tun a ranar Juma’ar da ta gabata ne aka fara yin gwanjon ashanar da aka kiyasta kudin ta kan naira miliyan 17.6 wadda aka kamata tun a cikin watan Janairun wannan shekarar.

Ya ce, kananan ’yan kasuwa aka sayarwa kayan a kan kasa sosai da farashin da ake sayarwa a kasuwa, kuma an yi hakan ne domin kara sukakawa al’ummar kasa matsalolin tsadar rayuwa da suke fuskanta.

“Babban shugaban wannan hukumar ne ya bayar da umarnin sayar da kayan ga jama’a a matsayin wani bangare na magance matsalolin matsin rayuwa.”

Mr Oladeji ya ci gaba da bayanin cewa bisa yadda mutane suke ta tururuwa wajen sayen Ashanar, alama ce dake nuna gamsuwar al’ummar kasa a game da tsarin gwanjon kayayyaki da hukumar ta kwastam take yi a kasar.

Ya bayyana cewa a karshe bayan an kammala sayar da Ashanar, hukumar za ta saka kudaden cikin asusun tarayya ne.

Ya kuma yaba sosai bisa yadda hedikwatar ta kwastam ke baiwa ofishin shiyyar arewa maso yamma hadin kai wajen gudanar da aikinsa. (Garba Abdullahi Bagwai)