logo

HAUSA

Lin Lin: Taimakawa iyaye mata masu zaman gida wajen ba da gudummawa ga al’umma

2024-03-25 16:22:24 CMG Hausa


Lin Lin ita ce shugabar kungiyar iyaye mata masu zaman gida ta Nanxiang, wani gari dake yankin Jiading a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin. Kungiyar ita ce irinta ta farko a Shanghai. A lokacin kaddamar da ita a shekarar 2019, kungiyar tana da mambobi 80. Zuwa yanzu kuwa, tana da kusan mambobi 500. Karkashin jagorancin Lin Lin, mambobi mata da dama sun shiga ayyukan raya unguwannin jama’a a shekarun baya-bayan nan. Kana yayin da suke daukar  nauye-nauyen taimakawa al’umma, su ma sun samu cikar burikansu.

Kimanin shekaru 10 da suka gabata, Lin Lin da Ding Changhua, wato mijinta, na da wani kamfanin samar da kayayyakin gida a Shanghai. Amma hadarin mota ya sauya musu rayuwa. Lin Lin da danta Ding Hanming, sun jikkata yayin hadarin, inda aka kwantar da su a asibiti har tsawon fiye da shekara 1. Yayin da Ding Changhua yake jinyar Ding Hanming a asibiti, mata da dama dake makwabtaka da Lin Lin ne suka rika karba-karba wajen kula da ita. Hakika wannan yunkuri na matan ya taba zuciyar Lin Lin. Bayan an sallame ta daga asibiti, sai Lin Lin ta koma zaman gida domin ta kula da iyalinta. A sannan ne ta yi tunanin yadda za ta sakawa al’umma bisa kulawa da taimakon da aka ba ta.

A shekarar 2014, Lin Lin ta fara yayata koyawa yara karatu kai tsaye da ma ta kafar intanet, da bayar da shawarwari ga yara da iyayensu, domin taimaka musu wajen inganta kwarewarsu ta karatu. Shekaru biyu bayan nan, Lin Lin ta tara kudin bude wani dakin karatun littattafai masu hotuna a yankin Jiading, wanda ke ba jama’a damar zuwa a kyauta. Ta kan shirya tarukan karatun tatsuniyoyi a dakin.

Lin Lin ta bayyana cewa, “na shafe kusan shekara 1 ina karanta littattafai masu hotuna tare da yarana. Karatun yana sanya ni cikin wani yanayi na nutsuwa da kwanciyar hankali. A shekarar 2016, na kai diyata Ding Zixuan domin ta shiga wani shiri a Shanghai, wanda ke da nufin karfafawa iyaye gwiwar yin karatu tare da ’ya’yansu. Ta wannan shirin, iyaye da dama sun fahimci muhimmancin yin karatu tare da ’ya’yansu.” Cikin shekaru 8 da suka gabata, Lin Lin ta shirya shirye-shiryen karatu tsakanin yara da iyayensu sama da 100, inda masana a fannin suka gabatar da shawarwari ga yara da iyayensu, domin inganta kwarewarsu ta karatu. Iyayen ma sun gabatar da nasu shawarwari kan yadda za a kyautata samarwa ’ya’yansu ilimi. Haka kuma, ta wallafa bayanai a kafar intanet, game da litattafan yara daban-daban, wadanda suka ja hankalin dubban masu karatu a kan intanet. Ta hanyar shirye-shiryen, ta samu damar haduwa da iyaye mata da dama masu zaman gida.

A shekarar 2018, Lin Lin ta kafa wani rukunin tattaunawa wato Group, inda ita da iyaye mata sama da 80 kan tattauna kan batutuwan da suka shafi karatu da ilimin iyali da dangantakar dake tsakanin iyaye da yaransu. A kai a kai, matan kan shirya shirye-shirye domin inganta zaman lafiya da jituwa tsakanin mazauna unguwanni. Yayin da take kokarin ganin cimma burinta ta hanyar bayar da gudummuwa, Lin Lin ta yi farin cikin ganin ta taimakawa mabukata.

Da shekara ta zagayo, sai Lin Lin da sauran wasu mata da dama suka kafa kungiyar iyaye mata masu zaman gida a garin Nanxiang, karkashin jagorancin kungiyar mata ta wurin. Lin Lin ta yi fatan ta wannan kungiya, iyaye mata za su kara fahimtar cewa, su ’yan wadannan unguwannin jama’a ne, musamman yayin da suke kara sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na raya unguwannin nasu.

Cikin kankanin lokaci, Lin Lin da tawagarta suka kafa kungiyar ’yan sa kai, wadda ta tsarawa mata masu zaman gida hanyoyin bayar da hidima, ciki har da aikin rarraba shara da karfafa ayyukan da suka shafi kandagarki da dakile yaduwar cutar COVID-19.

A shekarar 2019, garin Nanxiang ya fara daukar mata ’yan sa kai, wadanda suke bada kulawa da koyar da yara marasa galihu. Cikin shekarun da suka gabata, Lin Lin ta shigar da gomman iyaye mata cikin shirin.

A matsayinta na shugabar cibiyar kula da walwalar iyalai ta Yuelihui ta yankin Jiading, cikin shekarun da suka gabata, Lin Lin ta jagoranci ma’aikatan cibiyar wajen gudanar da ayyuka da dama na inganta karatu tsakanin yara da iyaye, da karatu tsakanin matasa, da kuma tsakanin manyan mata.

Lin Lin ta furta cewa, “baya ga mata masu zaman gida, mata da dama a yankin Jiading, ciki har da ma’aikata na gida da na kananan ofisoshi, sun shiga shirye-shiryen inganta walwalar al’umma a baya bayan nan. Ciki har da wandanda suka yi niyyar taimakawa mazauna wajen inganta ilimi tsakanin iyali. Mata da dama, wadanda a baya suka mai da hankali kan kula da iyalinsu kawai, sun taka muhimmiyar rawa wajen kyautata harkokin unguwanninsu na al’umma.”

Lin Lin ta yi imanin cewa, al’ummar Sinawa na kara dunkulewa, mata kuma suna iya zabar tsarin rayuwar da suke so da kansu, lamarin dake nufin za su iya fita su yi aiki ko su zabi zaman gida. Bisa la’akari da gudummuwar da suke bayarwa wajen kyautata gina unguwannin zamansu, ana girmama mata masu zaman gida. Wannan ya nuna cewa, matan kasar Sin suna da tarin zabuka a wannan zamani.

Bisa ayyukan Lin Lin, za a iya cewa, ta hanyar shiga ayyukan tafiyar da harkokin unguwannin, mata masu zaman gida na iya bayar da gudunmuwa wajen inganta zaman jituwa da kwanciyar hankali da wadata a cikin al’umma. (Kande Gao)