logo

HAUSA

Mutane 4 da ake tuhuma da harin ta’addanci a Rasha ’yan Tajikistan ne

2024-03-25 14:20:14 CGTN HAUSA

 

Kafar yada labarai ta kasar Rasha ta ce mutane 4 da ake tuhuma da aikata laifin bude wuta a wani dakin kide-kide a Rasha ’yan kasar Tajikistan ne. Kazalika, da safiyar yau Litinin kotun binciken manyan laifuffukan yankin Basmanny na birnin Moscow, hedkwatar kasar Rasha, ta ba da umarnin tsare su domin yanke musu hukunci.

Ofishin watsa labarai na kotun ya ce Dalerdzhou Mirzoev, da Rachabalizoda Saidakrami sun amince da laifinsu. Mirzoev mai shekaru 32 da haihuwa, da Saidakrami mai shekaru 30 da haihuwa, mambobin kungiyar fafutuka ne, yayin da Shamsidin Fariduni mai shekaru 23 da haihuwa tsohon ma’aikaci ne a birnin Podolysk dake dab da Moscow. Sai kuma Muhammadsobir Fayzov mai shekaru 19 da haihuwa, wanda ya taba aikin wanzami ne a birnin Ivanovo dake arewa maso gabashin kasar.

Rahotanni na cewa, a jiya Lahadi, wadannan mutane 4 sun amsa laifinsu a hedkwatar kwamitin binciken laifuffuka. Kwamitin ya zarge su da laifin aikata harin ta’addanci da kisan mutane. Idan an tabbatar da laifinsu, za a iya yanke musu hukuncin daurin rai da rai. (Amina Xu)