logo

HAUSA

Wajabcin kara zuba jari da huldar bangarori daban daban domin kawo karshen tarin fuka ko babban tari

2024-03-25 09:02:11 CMG Hausa

A ranar jiya ce, Lahadi 24 ga watan Maris din shekarar 2024, ministan kiwon lafiya na kasar Nijar ya gabatar da jawabi a albarkacin ranar duniya ta yaki da cutar tarin fuka ko babban tari, ganin cewa ita ma kasar tana fama da wannan annoba.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Kamar sauran kasashen duniya, kasar Nijar ta yi bikin ranar jiya a matsayin ranar kasa da kasa ta yaki da tarin fuka ko babban tari, bisa taken muna iyar kawo karshen cutar tarin fuka.

Ranar ta kasance wata dama ta wayar kan al’umma game da illolin kiwon lafiya, na jama’a da na tattalin arziki na wannan cuta domin kara yawaita ayyukan da za su taimaka wajen kawar da wannan annoba a duniya.

A albarkacin ranar ce, ministan kiwon lafiya, kanal manjo Garba Hakimi da ya isar da sako, ya bayyana cewa zabin wannan take na cike da makoma mai haske. Ganin cewa, ana iya dakatar da yaduwar tarin fuka ko babban tari, ta hanyar janyo hankalin shugabanni, kara zuba jari, amincewa da sabbin sauye-sauye da kuma huldar bangarori daban daban.

Shekara ta 2024, shekara ce ta daukar niyya domin ingiza yaki domin raba duniya da wannan cuta, in ji ministan kiwon lafiya.

A Nijar, a cewar kanal manjo Garba Hakimi, tarin fuka ko babban tari na kasancewa matsala ta kiwon lafiya. Tsarin daukar nauyin cutar na kasa ya taimaka wajen shirin kasa na yaki da babban tari ko tarin fuka tare da samun sakamako mai gamsarwa. Aikin gwaji ya samu ci gaba da wuce dubu 14 da 646 a shekarar 2022 zuwa dubu 15 da 743 na nau’in cutar a shekarar 2023, in ji ministan kiwon lafiya na Nijar kanal manjo Garba Hakimi.

Mamane Ada, sashen Hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.