logo

HAUSA

An kammala gasar wanni ta Afrika karo na 13 inda Masar ta kankane teburin lambobin yabo

2024-03-24 21:35:07 CMG Hausa

An kammala gasar wasannin kasashen Africa karo na 13, jiya Asabar a Accra babban birnin kasar Ghana, inda Masar ta kankane teburin lambobin yabo.

Masar ta samu lambobin zinare 101 a wasannin, yayin da Nijeriya ke bi mata baya da lambobin zinare 47, sai Afrika ta Kudu da ta samu 32. 

Mai masaukin baki kasar Ghana kuma, ita ce ta zo na 6, inda ta samu lambobin zinare 19.

Yayin rufe gasar, shugaban Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya taya murna tare da yabawa dukkan ‘yan wasan bisa jajircewarsu da jarumta da sadaukarwa, domin lashe lambobin yabo ga kasashensu.

Za a gudanar da zagaye na gaba na wasannin ne a shekarar 2027 a birnin Alkahira na kasar Masar. (Fa’iza Mustapha)