logo

HAUSA

Putin ya lashi takobin hukunta wadanda ke da hannu a harin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 133 a Moscow

2024-03-24 16:55:49 CMG Hausa

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya lashi takobin hukunta wadanda ke da hannu a harin da aka kai kasarsa ranar Juma’ar da ta gabata, harin da ya bayyana a matsayin na ta’addanci da rashin imani.

Vladimir Putin ya bayyana haka ne jiya Asabar a jawabin da ya yi wa al’ummar kasar ta kafar Talabijin. 

Kwamitin bincike na kasar Rasha ya bayyana a jiya cewa, mummunan harin na bindiga da aka kai dandalin wasanni dake wajen birnin Moscow a ranar Juma’a, ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 133 da jikkatar wasu sama da 100.

Da farko, kafafen watsa labarai sun ruwaito cewa adadin wadanda suka mutu ya kai 143.

Bayan aukuwar harin, an tsaurara matakan tsaro a fadin kasar ta Rasha.

Fadar White House ta shugaban Amurka ta bayyana a ranar Juma’a da dare cewa, babu wata alama ko alamu dake nuna cewa kasar Ukraine ko ‘yan kasar na da hannu a harin, tana mai cewa, za ta ci gaba da sa ido kan lamarin.

Sai dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen Rasha, Maria Zakharova ta ce furucin na Amurka ya haifar da tarin tambayoyi, tana mai bukatar Amurkar da ta gabatar da kwararan bayanai ga Rasha.

Shi kuma mashawarcin ofishin shugaban kasar Ukraine Mikhai Podolyak da ma’aikatar harkokin wajen kasar, sun yi watsi da zargin cewa Ukraine na da hannu a harin.

A nasa bangare, Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya yi tir da harin. Kana ya jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su da al’umma da gwamnatin Rasha. Su ma shugabannin kasashe a fadin duniya, sun jajanta tare da yin tir da harin. (Fa’iza Mustapha)